Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Atletico Madrid na neman Rashford, Liverpool za ta haƙura da Frimpong
Atletico Madrid za ta iya ɗaukar aron ɗan wasan gaban Manchester United da Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27, wanda ke fama da rashin tagomashi a Old Trafford. (TBR Football)
Ƙungiyoyi a Saudiyya ma suna sha'awar Rashford inda suke ganin shi ne ɗan wasan da zai iya ƙara bunƙasa darajar gasar ƙasar a duniya. (Telegraph)
Liverpool za ta haƙura da zawarcin ɗan wasan baya na Bayer Leverkusen da Netherlands Jeremie Frimpong, mai shekara 24, idan Alexander-Arnold ya bar ƙungiyar saboda koci Arne Slot zai fi son ɗan wasan baya na gefen dama, wanda ya fi kyau a tsaron baya, kuma yana ganin Frimpong bai dace da hakan ba. (Florian Plettenberg/Sky Germany)
Liverpool ta yi wa ɗan wasan baya na ƙasar Ingila Trent Alexander-Arnold, mai shekara 26, tayin sabon kwantiragi, amma Real Madrid za ta ƙara ƙaimi wajen neman ɗaukar ɗan wasan a cinikin kyauta a bazara mai zuwa inda ta ke shirin ganawa da shi a watan Janairu. (Caught Offside)
Manchester City na zawarcin ɗan wasan bayan Crystal Palace da Ingila Marc Guehi, mai shekara 24 a matsayin a wani ɓangare na garambaul ɗin da za ta yi a jerin ƴan wasan bayanta. (Football Insider)
Arsenal na nazarin ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila Kiernan Dewsbury-Hall, mai shekara 26, a watan Janairu. (Caught Offside)
Crystal Palace da Leicester da Wolves duk suna rububin ƙarɓar aron ɗan wasan Newcastle da Paraguay Miguel Almiron, mai shekara 30, a watan Janairu. (Sun)
Manchester City na tunanin zawarcin ɗan wasan gaba na Brighton da Jamhuriyar Ireland Evan Ferguson, mai shekara 20, wanda ke fuskantar rashin tagomashi a filin wasan Amex, inda ya ci ƙwallo ɗaya kacal a kakar wasan bana. (GiveMeSport)
Fulham ma tana sha'awar Ferguson inda ta ke son ɗaukar shi a matsayin aro zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana. (Independent)
Manchester United na ci gaba da zawarcin ɗan wasan baya na ƙasar Portugal Nuno Mendes mai shekara 22, wanda Paris St-Germain ke neman tsawaita kwantiraginsa zuwa 2026. (Florian Plettenberg/Sky Germany)
Ɗan wasan baya na Inter Milan da Italiya Federico Dimarco, mai shekara 27, zai yi watsi da duk wani tayi daga Manchester United domin ci gaba da zama da zakarun na Serie A. (Tuttosport)
Ƙungiyoyin Premier suna rububin ɗan wasan gaban Faransa Randal Kolo Muani, mai shekara 26, bayan da Paris St-Germain ta sanya ɗan wasan a kasuwa. (Times)