Nwaneri ya shiga jerin ƴan wasan gaba na Arsenal masu jinya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal na cin karo da koma baya, sakamakon da ƴan wasan gabanta da yawa ke kara jin ciwo, na bayan nan shi ne Ethan Nwaneri.

Ɗan wasan zai yi jinya zuwa karshen watan Janairu, bayan da ƙungiyar ke shirin karawa da Newcastle United a Carabao Cup a daf da karshe a Emirates

Matashi, Nwaneri, mai shekara 17, ya buga wa Gunners wasa na biyu a Premier League a bana, inda Brighton da Arsenal suka tashi 1-1, kuma shi ne ya fara cin ƙwallon.

Nwaneri ya samu buga wasan na ranar Asabar, sakamakon da Bukayo Saka ke jinya, wanda ake cewa sai cikin watan Maris zai koma taka leda - Raheem Sterling ma na jinya.

Mikel Arteta zai yi wasa shida da suka rage masa a Janairu ba tare da matashin ba, har da wanda Gunners za ta karɓi bakuncin Newcastle a Carabao Cup ranar Talata.

Watakila Kai Havertz zai buga wa Arsenal wasa da Newcastle, bayan da ɗan kasar Jamus bai yi karawa da Brentford da kuma Brighton ba.

Martin Odegaard bai da lafiya, amma ya fara da zaman benci a wasan da Gunners ta tashi 1-1 a gidan Brentford ranar Asabar a Premier League.

Arteta ya sanar cewar takwas daga fitattun ƴan wasansa ba su je atisaye ba ranar Litinin.

Arsenal tana ta biyun teburin Premier League da tazarar maki shida tsakani da Liverpool mai jan ragama da kwantan wasa ɗaya.