Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaya Man City za ta kasance idan ba Erling Halland?
Kusan a ce ba a bayar da wani muhimmanci ba ga kasancewar Erling Haaland a Manchester City a wannan lokaci da ƙungiyar ke fuskantar ƙalubale da koma-baya a wasanninta - lamarin da a yanzu ya miƙa har zuwa wata huɗu.
Rashin ɗangaban na Norway a tawagar Man City ba shi ne dalilin rashin ƙoƙarin ƙungiyar ba har ta sha kashi 3-1; matsalarsu ta wuce haka nesa ba kusa ba.
Tun da daɗewa aka ga hakan inda yanzu ta bayyana cewa tsakiyarsu ta tsufa - kamar yadda shi kansa kociyansu, Guardiola ya ambata da bakinsa - 'yanwasan sun yi rauni ba su da kuzari kuma 'yanbaya na fama da rauni.
Ƙari a kan waɗannan matsaloli tunanin 'yanwasan ya yi rauni kuma sun gaji.
Kusan a ce sai dai su sanya wa Haaland ƙwallon a kwano idan a ce abinci ne sannan ya ci - ma'ana sai dai su gyara ƙwallon su yi tankaɗe da reraya su sannan su miƙa mishi ya zura ta a raga kawai.
Haaland ba ɗanwasa ba ne kamar Cristiano Ronaldo da Lionel Messi a lokacin ganiyarsu ko kuma a yanzu kamar Kylian Mbappe, waɗanda za su iya sauya yanayin wasa ta hanyar nemo ƙwallon daga wajen da'ira su nuna wata bajinta ko gwaninta har ta kai su sa ta a raga.
To amma dai duk da haka yana sa 'yanbaya aiki sosai ba sa sakewa da shi a kusa. Sai dai ba a kodayaushe ba ne hakan ke yin tasiri - amma duk da haka ba abu ne da za a kawar da ito a kansa ba duk da cewa Cityn na cikin matsala - tun da jimawa suka fitar da rai a kan gasar Premier ta bana kuma yanzu an yi waje da su daga gasar Turai ma - duk da haka Haaland yana da ƙwallo 27.
To abin tambaya a nan shi ne : idan ba Haaland a yanzu me zai rage ga Man City?
A ranar Laraba da daddare a babban birnin Sifaniya Madrid a iya cewa an ga amsar wannan tambaya.
'Yanwasan sun gaji ba su da kataɓus ba ƙwazo hasali ma ana ganin sun yi sa'a da suka jefa ɗaya ma a raga.
Guardiola ya ce raunin da Haaland ya ji a wasansu da Newcastle ranar Asabar ba wani mai tayar da hankali ba ne - nan gaba kaɗan zai koma fage - wannan labari ne mai daɗin ji ga City, domin idan ba Haaland sai a ce ta ƙare musu ƙarƙaf domin zai yi wuya su samu damar takarar gasar zakarun Turai ta gaba a matsayin da suke yanzu a Premier - su ɗore matsayi na huɗu - maki ɗaya kacal a gaban ta biyar da ta shida.