Liverpool ta gwada wa Man United ƙwanji a Premier League

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United ta yi rashin nasara 3-0 a hannun Liverpool a wasan mako na uku a Premier League da suka kara a Old Trafford ranar Lahadi.

Luis Diaz ne ya fara cin United ƙwallo biyu tun kan hutu, kuma Mohamed Salah ne ya bayar da dukkan biyun da aka zura a raga.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Salah ɗan wasan tawagar Masar ya kara na uku a karawar ta hamayya.

Kenan Salah ya ci ƙwallo 10 ya bayar da shida aka zura a raga a karawa 22 a Premier League da Liverpool ta fuskanci Manchester United

Kociyan Liverpool, Arne Slot ya zama na farko da ya ci wasa uku a jere da fara kakar Premier League ba tare da an zura musu ƙwallo ba, tun bayan bajintar Sven-Goran Eriksson a Manchester City a 2007.

Da wannan sakamakon Liverpool ta haɗa maki tara a wasa uku da fara kakar bana, bayan da ta fara cin Ipswich Town 2-0 ranar 17 ga watan Agusta da doke Brentford 2-0 ranar 25 ga watan Agusta.

United kuwa maki uku ne da ita a wasa uku a Premier, inda ta fara cin Fulham 1-0 ranar 16 ga watan jiya, sai rashin nasara 2-1 a gidan Brighton ranar 24 ga watan Agusta.

Ƙungiyar Old Trafford za ta je gidan Southampton ranar 14 ga watan Satumba a karawar mako na huɗu a Premier League.

Ita kuwa Liverpool za ta karbi bakuncin Nottingham Forest a ranar ta 14 ga watan Satumba a babbar gasar tamaula ta Ingila a Anfield.

Waɗanda suka ci ƙwallaye da yawa a Old Trafford tun daga 24 ga Janairun 2021

Ƙwallo 31 - Marcus Rashford

Ƙwallo 29 - Bruno Fernandes

Ƙwallo 17 - Cristiano Ronaldo

Ƙwallo 13 - Scott McTominay

Ƙwallo 10 - Mohamed Salah

Ƙwallo 10 - Anthony Martial