Arsenal ta samu kuɗin shiga da yawa amma ta yi hasarar £17.7m

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal ta sanar da samun £616.6m, amma ta yi hasarar £17.7m a zangon kasuwanci zuwa 31 ga watan Mayun 2024.

Gunners ta koma buga Champions League a 2023/24 da kai wa kwata fainals, hakan ya sa ta samu karin £71.1m wajen nuna wasanta a talabijin da karin kuɗin shiga sitadiya £29.1m.

Ƙungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama tana ta biyu a teburin Premier League, yayin da ƙungiyar mata ta Arsenal take ta ukun teburi a Women Super League da lashe League Cup.

Karin ƙudin shiga da ta samu kaso 32.1 cikin 100 ne daga £466.7m da ta sanar a Mayun 2023.

Yayin da hsarar £17.7m kafin a kwashe haraji kaso 66 cikin 100 ne, kasa da hasarar £52.1m a gabaki ɗayan 2022-23.

Bayan da Gunners ta koma buga gasar zakarun Turai ta samu karin £262.3m daga £191.2m wajen nuna wasanta a talabijin da kuma £102.6m daga £131.7m a kallon wasanni a sitadiya.

Arsenal ta samu riba wajen sayar da ƴan wasa da bayar da wasu aro da ya kai £52.4m daga £12.2m, an samu karin cajin kasuwanci £6.2m daga £18.4m.