Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An dage wasan Arsenal da Man City saboda fafatawa da PSV
An dage wasan da Arsenal za ta yi da Manchester City a gasar Premier League ranar 19 ga watan Oktoba, domin ta kara da PSV a Europa League.
Hakan ya biyo bayan bai wa Gunners damar buga Europa League da PSV Eindhoven.
An dage wasan da Gunners ya kamata ta kara da PSV ranar Alhamis, hakan ya biyo bayan zaman makokin rasuwar Sarauniya Elizabeth II.
Uefa ta hangi za a yi karancin jami'an tsaro da mutanen da za su gudanar da wasu ayyukan, shi ya sa ta dage fafatawar.
Arsenal za ta karbi bakuncin kungiyar Netherlands ranar 20 ga watan Oktoba.
Hukumar da ke gudanar da Premier League ta ce za ta sanar da ranar da kungiyoyin biyu za su fuskanci juna nan gaba.
An dage dukkan wasannin babbar gasar tamaula ta Ingila a makon jiya, bayan rasuwar Sarauniya Elizabeth II.
Haka kuma an kara dage wasu fafatawa uku da ya kamata a kara a makon nan, saboda shirin binne Sarauniya ranar Litinin.
Wasannin da aka soke sun hada da wanda Chelsea za ta karbi bakuncin Liverpool da wanda Leeds za ta ziyarci Manchester United.
Tuni aka dage wasan Brighton da Crystal Palace, bayan da kungiyar ma'aikatan jirgin kasa ke shirin yin yajin aiki.
Jadawalin wasanni Premier League na kara fuskantar kalubale a kakar nan, bayan da za a dakatar da gasar sakamakon fafatawar cin Kofin Duniya da za a yi a Qatar tsakanin 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disamba.