Batun daukar Rabiot zuwa Man United ya bi ruwa

An wallafa

Shirin da Manchester United ke yi kan daukar dan kwallon Faransa, Adrien Rabiot daga Juventus ya bi ruwa.

United ta so daukar dan wasan mai shekara 27 domin ta kara karfafa gurbin masu buga mata tsakiya.

Tun farko sun cimma yarjejeniya kan cinikin, anma albashi ya kawo tsaiko kan bukatar Rabiot da kudin da United ke son dunga biyansa.

An dauka tun farko United za ta dauki dan kwallon a matakin wanda zai ke karbar albashi mafi tsoka tsakanin 'yan kwallon kungiyar.

Watakila a sake tayar da maganar cinikin kan a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon kafa ta Turai da ke ci a yanzu haka.

Rabiot ya koma Juventus a matakin wanda bai da kungiya a 2019, yanzu saura kwantiragin kaka daya ya rage masa a kungiyar da ke buga Serie A.

Har yanzu United ba ta fitar da ran sayen dan kwallon tawagar Netherlands mai taka leda a Barcelona, Frenkie de Jong ba, koda yake kungiyar Sifaniya ta sanar a makon jiya cewa De Jong zai ci gaba da taka leda a Camp Nou.

United tana karshen teburi, bayan shan kashi a wasa biyu a jere da ta yi da Brighton da kuma Brentford a gasar Premier ta bana.