Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hanyoyin da likitoci suke bi wajen yi wa al'aurar mata kwaskwarima
Wata likitar mata a Najeriya ta bayyana hanyoyin da suke bi wajen yi wa al'aurar mata kwaskwasrima yadda za su ji dadin jima'i.
A tattaunawarta da BBC Hausa, Dr Anisa Umar Ambursa, ta ce suna kuma gyara al'aurar mata domin ta yi kyawun gani idan mace ba ta jin dadin yadda take.
"Akwai yadda muke bi mu ciccibo ta...idan akwai wani gefe da ba ta ji dadinsa ko tana jin kunya wajen saduwa, akwai yadda muke yi mu gyara shi," in ji ta.
Dr. Anisa ta ce suna amfani da allurori da kuma 'yar gajeruwar tiyata wajen gudanar da ayyukansu ta yadda "mata za su kara yin ni'ima."
Ta ce mata da dama suna fuakantar kalubale a al'aurorinsu musamman wadanda aka yi wa kaciya ko fyade, tana mai cewa hakan ne ya sa suke bukatar kwaskwarima domin gyara kansu.