Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Copa del Rey: Barca da Sociedad a daf da na kusa da na karshe
Barcelona za ta fafata da Real Sociedad a Copa del Rey wasan daf da na kusa da na karshe a Camp Nou ranar Laraba.
Barcelona ta kawo wannan matakin bayan doke Intercity 4-3 a bugun fenariti da kuma cin Ceuta 5-0.
Ita kuwa Sosiedad wadda ba ta buga Spanish Super Cup ba ta yi nasara a kan Cazalegas da 4-1 ta doke Coria 5-0 da cin UD Logrones 1-0.
Wannan shi ne karon farko tun 2016/17 da za su fuskanci juna a kofin, bayan da suka hadu gida da waje,, shima a quarter finals.
A lokacin karkashin Luis Enrique, Barca ta ci 1-0 a Anoeta, sannan ta zura 5-2 a Camp Nou.
Sun kuma fafata a 2013/14 a daf da karshe a Copa del Rey, inda Barca ta yi nasara a kan Sociedad da ci 3-1 gida da waje.
A kakar nan Barcelona ta je Sociedad ta ci 4-1 ranar 21 ga watan Agustan 2022 a gasar La Liga.
Barcelona ce kan gaba a yawan lashe Copa del Rey mai 31 jumulla, Real Sociedad tana da uku a tarihi.
A cikin watan Janairun 2023 Barcelona ta lashe Spanish Super Cup a Saudi Arabia, bayan cin Real Madrid 3-1 ta dauki kofin farko a bana.