Arsenal za ta sayar da Jesus kuma ta na zawarcin Onana, Man Utd ta fasa korar Ten Hag

An wallafa

Arsenal ta shirya tsaf wajen sauraron tayin da za a yi wa dan wasan gaban kungiyar da kuma Brazil Gabriel Jesus mai shekara 27 a bazara. (Athletic - subscription required)

Haka kuma Gunners na fatan dan wasan tsakiyar Italiya Jorginho, mai shekara 32, zai yi watsi da zawarcin da Juventus da Lazio da kuma Napoli su ke yi masa domin ya tsawaita kwantaraginsa da su. (Standard)

Brighton na son ta dauko Kieran McKenna daga Ipswich Town idan kocinta Roberto de Zerbi ya bar kungiyar a karshen kakar wasanni. (Guardian)

Tottenham na zawarcin dan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila Conor Gallagher, dan shekara 24, tare da dan wasa mai kai hari na Feyenoord da Mexico Santiago Gimenez mai shekara 23 a wannan bazarar, yayin da kuma suke son dan wasan bayan Bournemouth da Ingila Lloyd Kelly mai shekara 25. (Telegraph - subscription required)

Watakila a tilastawa Everton sayar da golan Ingila Jordan Pickford, mai shekara , 30, idan tattaunawar da suke yi da wadanda suke yi da kamfanin 777 da ke son ya mallaki kungiyar ta ruguje. (Talksport)

Arsenal da Bayern Munich da Newcastle na cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan tsakiya na Everton da Belgium Amadou Onana, dan shekara 22. (Football Transfers)

Manchester United na shirin ci gaba da kasancewa da kocinta, Erik ten Hag a kakar wasan da ke tafe saboda ba ta da wani zabi kuma idan ta kori dan kasar Netherlands to sai ta kashe makudan kudade.. (Athletic - subscription required)

Dan wasan tsakiya na Manchester United da Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 29, ya ce makormarsa a Old Trafford ta dogara ne akan ko kungiyar ta na son ya ci gaba da taka mata leda har bayan bazara. (Telegraph - subscription required)

Newcastle United ba za bada kai ba wajan sayar da dan wasan tsakiya na Brazil Bruno Guimaraes mai shekara 26 kan kudi kasa da fam miliyan 100 ko rabuwa da dan wasa mai kai hari na Sweden Alexander Isak, dan shekara 24. (i Sport)

Newcastle na son daukar mai tsaron bayan Fulham da Ingila Tosin Adarabioyo mai shekara 26 (Sun)

Adarabioyo, wanda AC Milan da Manchester United da Liverpool, suke zawarcinsa ya fadawa Fulham cewa ba za isa hannu a wani sabon kwantaragi ba idan wanda yake aiki a karkashinsa ya zo karshe a bazara. (Mail)

Borussia Dortmund na tunanin dawo da tsohon kocinta Jurgen Klopp a 2025 bayan kocin Liverpool ya bar Anfield a karshen kakar wasa ta bana . (Independent)

West Ham na fatan dan wasan tsakiya na kasar Ghana Mohammed Kudus dan shekara 23 da dan wasan tsakiya na Brazil Lucas Paquet mai shekara 26 tare da dan wasan tsakiya na Mexico Edson Alvarez mai shekara 26, za su nemi zuwa wasu kungiyoyi a bazara. (Football Insider)

Fluminense ta gabatar da kudurin sayan mai tsaron bayan Brazil Thiago Silva bayan da dan wasan mai shekara 39 ya sanar cewa zai bar Chelsea a karshen kakar wasa ta bana. (Fabrizio Romano)

Mataimakin kocin Feyenoord Sipke Hulshoff da shugaban kula da yadda 'yan wasa ke taka leda Ruben Peeters da Etienne Reijnen duk sun amince su bi kocinsu Arne Slot zuwa Liverpool. (Football Insider)

Everton na zawarcin dan wasan tsakya na Hull City da Ingila Jacob Greaves dan shekara 23, da kuma dan wasan gaban Blackburn Rovers da yankin Ireland Sammie Szmodics, mai shekara 28. (Football Transfers)

Juventus da AC Milan sun dakatar da zawarcin da suke yi wa Joshua Zirkzee saboda fargabar cewa dan wasan gaba na Bologna da Netherlands mai shekara 22 ya fi son ya koma taka leda a Arsenal a wannan bazara. (Givemesport)

Dan wasan bayan Barcelona da Uruguay Ronald Araujo, mai shekara 25, na shawara akan ko ya Sanya hannu akan wani sabon kwantaragi da kungiyar ta Safaniya yayin da Manchester United da Bayern Munich ke zawarcinsa. (Sport - in Spanish)