Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa aka samu sauyin sheƙa daga APC zuwa wasu jam'iyyu a Bauchi?
Wasu 'yan jam'iyyar APC a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya na ci gaba da ficewa zuwa wasu jam’iyyu sakamakon zargin cewa ana yi musu ɗauki-ɗora da kuma nuna bambanci a tsakaninsu.
Hakan na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da yaƙin neman zaɓe a sassan Najeriya gabanin manyan zaɓukan ƙasar da za a yi a watannin Fabrairu da Maris ɗin 2023.
Jiga-jigan APC a Bauchin musamman waɗanda ba su gamsu da yadda aka gudanar zaɓen fitar da gwanin jam'iyyar ba ne suke sauya sheƙar.
Wannan ya sa wasu na ganin hakan barazana ne ga yunƙurin da APC ke yi na karɓe mulki daga hannun PDP.
Ga alama wannan ƙurar da ta tashi tun lokacin da aka kammala zaɓen fitar da gwani a APC a Bauchi har yanzu ba ta lafa ba, kasancewar rikici ya cukwuikuye jam'iyyar daga dambarwar wadanda suke ganin an kitsa kutungwilar da ta yi sanadin rashin samun takararsu, suna ci gaba da sauya sheƙa.
Alhaji Al-amin Sani Muhammad wadda ya nemi takarar gwamnan jihar Bauchi amma bai samu ba, yana daga cikin masu irin wannan korafi.
Ya ce “abin da ake zargin jam’iyyar APC ta jihar Bauchi da aikatawa a lokacin zaɓukan share fage ya shafe ni matuƙar shafa saboda munafunci da aka yi na sauya sunayen daliget a lokacin.
“Ni ban kai ƙara kotu ba saboda ba a kai jam’iyya kotu, to waɗansu su ma da suka ga ba za su je kotu ba sai suka zaɓi fita, wasu kuma suna ciki amma har yanzu cikin ƙunci suna sauraoron ko za a yi magana da su.
“To kuma muna shawarwari da mutanenmu mu ga mece ce makomarmu. Don haka shugabanin jam’iyyar APC a Bauchi babu lafiya ba sa ƙaunar jam’iyyar ba sa buƙatar ta kai ga nasara,” in ji shi.
End of Wasu labaran da suka shafi Jihar Bauchi
Sanatoci uku na jam’iyyar APC a Bauchi dai, sun sauya sheƙa zuwa NNPP da PDP, sannan ‘yan majalisar wakilai da dama su ma sun fice tuntuni.
Honorabul Ibrahim Makama na daga cikinsu inda ya koma PDP amma daga baya ya sake koma APC ɗin.
“Ni ban ma bari an zo an yi takarar fitar da gwani da ni ba. Na zo na nuna sha’awata ƙwarai da gaske amma ban tsaya ma ra’ayin zaɓen ba, sai na haƙura da shi saboda wasu dalilai.
“Kuma Ɗan Makama bai bar APC ba, ya dai tafiya ziyara irin ta siyasa saboda wasu dalilai, kuma da na ga wasu abubuwa daban a ziyarar da na je sai na koma gidanmu na APC na ci gaba da harkokin a da ƴan uwana.
Alhaji Shehu Aliyu Musa shi ne dan takarar mataimakin gwamna a jam’iyyar APC, ya ce wannan al’amari al’ada ce ta siyasa ta baka raba dan siyasa da ƙorafi, amma a cewarsa shugabancin APC a Bauchi ya yi abin da ya dace ga dukkan mambobinsa.
“Waɗanda a yau aka wayi gari daga cikinsu sun bar jam’iyyar nan sun bari ne bisa ra’ayin kansu. Amma babu wani abu da jam’iyya ko ɗan takara ya yi musu a cikin wannan tafiya.
“Wannan ba wani sabon abu ba ne, dama an saba ganin haka a ko yaushe. Amma Alhamdulillah a halin yanzu, wasu daga cikinsu mun bi su har gida mun rarrashe su kuma sun gamsu da irin kalamanmu cewa Allah Shi ke bayarwa Shi ke hanawa.
“Tsakani da Allah waɗanda suka yi fushi suka tsallake, a yanzu ba mu san wani saura da ya yi takarar nan kuma ba ya tare da mu ba, domin mun bi su mun rarrashe su, jam’iyya da iyayen jam’iyya duk sun bi su sun rarrashhe su, har yau kuma suna tare da mu.”
Ya ƙara da cewa: “A wannan lokaci zaben fitar da gwani aka yi a gaban kowa, kuma bawan Allahn nan ya bi kowa da kowa gida ya rarrashe shi, tsakani da Allah ina roƙonsu su daure su zo mu ci gaba da wannan tafiya domin mu ceci jihar Bauchi.”
Sai dai duk da wannan jawabi na Alhaji Shehu Musa, akwai Alhaji Faruk Mustapha, ɗan takarar gwamna da ya faɗi a zaɓen fitar da gwani na APC da ya koma PDP har ma ya zama daraktan yaƙin neman zaɓen Gwamna Bala Muhammad.
Masana siyasa dai na kallon irin wannan dambarwa tamkar babu mai tsawatarwa ko lallashin wadanda suke jin an ɓata musu, abin da kuma zai iya yi wa jam'iyyar tarnaƙi wajen samun galaba, muddin shugabannin APCin ba su shiga tsakani tare da bikon wadanda suka fice din ba.