Makomar Pino, Mount, Pellegrini, Ake, Jutgla, Zakaria da Conte a kasuwar ƴan ƙwallo

An wallafa

Chelsea na neman sayen ɗan wasan tsakiyar Villarreal Yeremy Pino, 19, don maye gurbin ɗan wasan tsakiyar Ingila Mason Mount da ke shiga watannin ƙarshe na kwantiraginsa. Chelase kuma na neman Lorenzo Pollegrini, 27 ɗan wasan tsakiyar Roma. (Telegraph)

Inter Milan kuwa ta shirya son kwadaitar da ɗan wasan baya na Netherlands, Nathan Ake, 27 daga Manchester City. (Ekrem Konur on Twitter)

Arsenal ta nuna sha’awar sayen dan wasan gaban Bruges Feran Jutgla, 23. (Totofichajes)

Chelsea na shrin tattaunawa halin da Denis Zakaria ke ciki a kungiyar inda dan wasan tsakiyar Switzerland mai shekara 25 ya gaza fitowa a ƙarƙashin sabon manaja Graham Potter.(Fabrizio Romano)

Liverpool na iya duba yiwuwar sayen dan wasan gaban Belgium Jeremy Doku, 21 a Janairu, (Calciomercato - in Italian)

AC Milan na duba yiwuwar sayen dan wasan Chelsea Hakim Ziyech, 29 a watan Janairu. (Tuttomercatoweb - in Italian)