Mbappe ne kan gaba a samun kudin shiga mai tsoka a 2022 - Forbes

An wallafa

Mujallar Forbes ta wallafa cewar Kylian Mbappe shi ne dan wasan tamaula da yake kan gaba wajen samun kudin shiga mai tsoka a 2022 a duniya.

Karon farko bayan shekara tara da ba a samu ko dai Cristiano Ronaldo ko kuma Lionel Messi a matsayi na farko ba.

Forbes mai bincike da kididdigar kudi ta yi kiyashin cewar dan kwallon Paris St Germain da Faransa, mai shekara 23 ya samu $128m (£115.2m) a kakar nan.

Takwaran Mbappe a PSG, Lionel Messi shi ne na biyu da ya samu kudin shiga $120m (£108m) sai dan wasan Manchester United, Ronaldo na uuku mai $100m (£90m).

Neymar da Mohamed Salah suna cikin biyar din farko.

Neymar dan wasan PSG da tawagar Brazil , an kiyasta cewar ya samu $87m (£78.4m) a kakar 2022-23 shi kuwa dan kwallon Liverpool Salah da Masar ya hada $53m (£47.7m).

Wanda ya taba zama a mataki na baya ba daga tsakanin Ronaldo ko Messi ba, shi ne David Beckham a 2013.

Mbappe ya kai wannan matakin, bayan da ya saka hannu a PSG kan yarjejeniyar mai tsoka ta ci gaba da taka leda a kungiyar a watan Mayu.

A lokacin an yi ta hasashen cewar Real Madrid zai koma da taka leda.

Cikin jerin 'yan wasan da Forbes ta bayyana Haaland da Mbappe sune ke kasa da shekara 30.

Jerin 'yan wasan tamaula 10 da suka samu kudi mai tsoka a 2022 in ji Forbes

  • Kylian Mbappe            PSG      $128m (£115.2m)
  • Lionel Messi                 PSG      $120m (£108m)
  • Cristiano Ronaldo       Manchester United     $100m (£90m)
  • Neymar                         PSG     $87m (£78.4m)
  • Mohamed Salah          Liverpool        $53m (£47.7m)
  • Erling Haaland               Manchester City         $39m (£35.1m)
  • Robert Lewandowski  Barcelona       $35m (31.5m)
  • Eden Hazard                   Real Madrid   $31m (£27.9m)
  • Andres Iniesta                Vissel Kobe $30m (£27m)
  • Kevin de Bruyne          Manchester City        $29m (26.1m)