Mauludi, ranar haɗuwa don koyar da halaye da ɗabi'un Fiyayyen Halitta
Wani bangare na al'ummar Najeriya da ma sauran Musulmin duniya na bikin zagayowar ranar haihuwar Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammadu (S.A.W)
Da yawan Musulmai na shagali da nuna murna a duk rana irin wannan ta 12 ga watan Rabi'ul Awwal a kalandar Musulunci, da aka haifi Annabi Muhammadu.
Tuni dai gwamnatin Najerya ta ayyana ranar Laraba, 27 ga Satumban 2023 a matsayin hutu ga ma'aikatan kasar domin su je su yi bikin Mauludi a gida, wato zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad.
Hukumomin kasar sun yi kira ga Musulmai 'yan Najeriya su tsarkake zukatansu tare da nuna soyayya da hakuri da juriya wadanda suna daga cikin kyawawan dabi'un da Annabi Muhammad.
Shi ma wani malamin addinin Musulunci a jihar Kaduna, Sheikh Salihu Abdullahi Mai Baro-ta ya jaddada muhimmancin wannan rana wajen sanar da yara da matasa tarihin Annabi Muhammadu.



