Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Everton za ta dauki Maguire, PSG ta kusa kammala yarjejeniyar daukar Goncalo Ramos
Everton na kokarin shan gaban Tottenham da West Ham wajen daukar dan bayan Manchester United dan kasar Ingila Harry Maguire, mai shekara 30. (Football Insider)
Chelsea da Manchester City na kara yunkuri wajen daukar dan wasan gefen Crystal Palace dan kasar Faransa Michael Olise, duk da cewa akwai rudani kan kudin da za a biya don ya koma daya daga cikin kungiyoyin. (Mirror)
Paris St-Germain ta kusa kammala yarjejeniyar daukar dan gaban Benfica dan kasar Portugal, Goncalo Ramos mai shekara 22. (L'Equipe - in French)
Clement Lenglet, ya nuna wa Barcelona sha’awarsa na sayar da shi ga kungiyar Saudiya ta Al-Nassr, yayin da dan wasan dan kasar Faransa ke son komawa Tottenham, inda ya shafe kakar bara a matsayin aro. (Sport - in Spanish)
Chelsea na fatan musanya dan gaban Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 30, da dan gaban Juventus dan kasar Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 23, a wani ciniki da za a hada da dan wasa da kudi. (Star)
Manchester United na sanya ido a kan matsayin dan tsakiyar Bayern Munich dan kasar Jamus Leon Goretzka, mai shekara 28, wanda ta yi amanna baya cikin wadanda shugaban kungiyar ke son sayarwa. (Mail)
Aston Villa, na son bayar da fam miliyan 25, a matsayin kudin da za a sayi dan tsakiyar Leeds United Tyler Adams, mai shekara 24, inda suke jiran amsa, yayin da ita kuma Chelsea ke duba yiwuwar daukarsa. . (Mail)
Tottenham na tattaunawa a kan daukar dan gaban Argentina Alejo Veliz, mai shekara 19, a kan kudi fam miliyan 12, sannan kuma ta na nuna yiwuwar sakin mai tsaron ragar Faransa Hugo Lloris, da dan tsakiyar Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, da Tanguy Ndombele da kuma dan gefen Spaniya Bryan Gil. (Evening Standard)
Za a duba lafiyar dan gaban Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 26,kafin ya kammala koma wa Paris St-Germain daga Barcelona. (RMC Sport - in French)
West Ham da Nottingham Forest na taya dan wasan PSG mai shekara 21 Hugo Ekitike. (RMC Sport, via Mail)
Southampton za ta dauki Max Aarons, mai shekara 23 daga Norwich domin cike gibin Tino Tino Livramento. (Talksport)