Falasdinawan da sojojin Israi’la ke rushe musu gidaje

Falasdinawan da sojojin Israi’la ke rushe musu gidaje
An wallafa

Dubban Falasdinawa ne suka shiga halin fargaba cewa sojojin Isra’ila za su fitar da su daga gidajensu a kudancin Gabar Kogin Jordan.

A watan Mayu ne wata Babbar Kotu ta ƙaƙaba takunkumi na shirin korarsu don mayar da yankin na Masafer Yatta sansanin horar da sojojin Isra’ila.

Idan har aka ci gaba da korar mutanen, to shi ne zai zama mafi girman abin da aka yi a cikin gwamman shekaru.

Tuni Isra’ilar ta rushe gidajen da ba a ba da izinin gina su ba a Yammacin Kogin Jordan a hukumance.