Pochettino ya buƙaci magoya bayan Chelsea su ƙara haƙuri da shi

An wallafa

Mauricio Pochettino ya yi kira ga magoya bayan Chelsea kan halin da kungiyar ke ciki na kasa taka rawar da ta dace a bana.

Chelsea ta yi rashin nasara ranar Asabar a Stamford Bridge da ci 2-0 a hannun Brentford, hakan ya kai kungiyar mataki na 11 a kan teburin gasar Ingila.

Magoya bayan kungiyar sun yi wa 'yan wasan Chelsea a lokacin da suke fita daga fili ihu, bayan tashi wasa da Brentford, karo na uku da aka doke ta a Stamford Bridge a bana.

Tuni tsohon kociyan Tottenham da Paris St Germain ya fara fuskantar kalubale, bayan da Chelsea ta kasa komawa kan ganiya duk da fitattun 'yan wasan da ta saya da tsada.

Kociyan ya ce tuni suna sane da bacin ran da ke tare da magoya bayan Chelsea, amma dai akwai wasu abubuwan da suka sa kungiyar take wannan halin.

Da yake jawabi kan karawar kofin Carabao da Chelsea za ta yi da Blackburn ranar Laraba, ya ce ''ya kamata su ci gaba da mara mana baya, na san halin da ake ciki.''

''Magoya baya na sa ran mu ci wasannin mu, suna kuma nuna bacin ran da suke ciki, amma ya kara da cewa su ci gaba da mara mana baya da sa kwarin gwiwa.''

''Akwai abubuwan da suka sa ba ma yin kokari, sannan ba ma kan ganiya, wasu lokutan ba mu da sa'a ne.

''Daya daga cikin abin da ke taba mu shi ne jinya da Christopher Nkunku ke yi - fitatcen dan wasa ne da muka dauka domin ya riƙa ci mana kwallaye, sai ga shi yana jinya tun kafin fara kakar nan.

''A wasu wasannin muna taka rawar da ta dace, illa ba ma cin kwallaye, muna ɓarar da damarmakin da muke samu, amma muna wasa mai kyau.''

Pochettino ya kara da cewar idan Chelsea ta dauki Carabao Cup na bana, zai ɗan faranta ran magoya bayan kungiyar.

Kociyan ya kara da cewar zai mayar da hankali sosai wajen yadda zai dauki Carabao Cup da FA Cup a kakar nan, hakan zai saukaka aikinsa a kungiyar.