Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
West Ham ta fitar da Arsenal daga Carabao Cup na bana
Arsenal ta yi ban kwana da Carabao Cup a bana, bayan da ta sha kashi a gidan West Ham United da ci 3-1 ranar Laraba.
Wasan farko da Declan Rice ya fuskanci tsohuwar kungiyarsa West Ham, tun bayan da ya koma Gunners kan fara wasannin kakar nan.
Arsenal ta fara cin kanta ta hannun Ben White, inda kwallon ta wuce mai tsaron raga Aaron Ramsdale, wanda ya kama gola a karon farko tun Satumba.
Daga baya ne West Ham ta kara na biyu ta hannun Mohammed Kudus, sannan Jarrod Bowen ya ci na uku.
Daf da za a tashi wasan kyaftin din Arsenal, Martin Odegaard ya zare daya, kenan Gunners ta yi ban kwana da gasar kakar nan.
Rice, wanda ya koma Arsenal kan fam miliyan 105 daga West Ham ya shiga wasan, bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu.
Duk da haka bai hana tsohuwar kungiyarsa kai wa zagayen daf da na kusa da na karshe a Carabao Cup ba.
Karon farko da David Moyes ya ci Arsenal a League Cup a haduwa biyar, wanda ya yi rashin nasara yana kociyan Preston North End da karawa biyu a Everton da fafatawa daya a Wes Ham.
Arsenal, wadda take ta biyu a teburin Premier League na takara a Champions League, wadda za ta yi fatan lashe FA Cup a bana.