Me Tinubu zai yi da bashin kusan dala biliyan takwas da zai karbo?

An wallafa

Majalisar dattijan Najeriya ta amince da kudurin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na karbo bashin kudi kusan dala biliyan takwas ga kwamitocinta.

Bashin ya hadar da dala biliyan 7.8, da yuro miliyan 100 daga kasashen waje.

Tun da farko, shugaban ya rubutawa majalisar bukatar neman yin nazari da kuma amincewa da wuri - shirinsa na karbo bashin kasashen waje na tsakanin shekara ta 2022-2024 don gudanar da ayyukan raya kasa cikin hanzari a bangarori kamar samar da ababen more rayuwa da kula da lafiya da ilmi da kuma inganta tsaro.

Ko da yake, a wasikar da ya aikawa Majalisar Dattijan, Shugaba Tinubu bai fayyace abubuwa dalla-dalla da zai yi da kudaden ba.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce Najeriya, kasa mafi girman tattalin arziki a Afirka kuma mafi arzikin man fetur, tana dogaro ne a kan bashi saboda karancin kudaden haraji da kuma abin da take samu daga man fetur da take fitarwa, wanda shi ne babbar kafar da ke samar mata kudaden kasashen waje.

Ya ce Najeriya ta tara kudi a kasuwannin bayar da bashi na kasashen duniya ciki har da ta hanyar takardun lamuni na yuro da rance daga masu ba da bashi kamar Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka don tallafa wa kasafin kudin kasar.

"Bisa la'akari da matsalolin tattalin arzikin da kasar take ciki yanzu, abu ne da ya zama wajibi mu yi amfani da bashin na kasashen waje don cike gibin kasafin kudi da za a yi amfani da shi wajen gudanar da muhimman ayyukan raya kasa" Reuters ya ambato Tinubu na fada a cikin wasikar.

Bola Tinubu dai ya janye tallafin man fetur da ke ciwa gwamnatin kasar kudi a farkon hawa mulkinsa, duk da farin jinin tallafin ga mutane da yawa a Najeriya, musamman ganin yadda cirewar ta haddasa hauhawar farashi da tsadar rayuwa.

Ya ce gwamnati za ta yi amfani da kudaden tallafin man fetur da za a yi tattalinsu wajen samar da ababen more rayuwa da inganta harkokin ilmi da kula da lafiya da gina tituna da gadoji da kuma shimfida layukan dogo.

Haka kuma Tinubu ya bayyana burin bunkasa harkokin zuba jari, maimakon raja'a a kan bashi wajen gudanar da ayyukan gwamnatinsa.

Majalisar Dattijai da takwararta ta Wakilai sun amince da kwarya-kwaryan kudurin kasafin kudin naira tirliyan 2.176 da Shugaba Tinubu ya gabatar musu.

Shugaban ya gabatar da kwarya-kwaryan kasafin kudin ne, don gudanar da muhimman "al'amura cikin gaggawa" kamar tsaron kasa.

A baya-bayan nan, majalisar ministocin Najeriya ta amince da naira tirliyan 26.1 a matsayin kudurin kasafin kudin kasar na shekara mai zuwa, wanda Reuters ya ce an kebe kashi daya cikin uku na kasafin a matsayin kudin biyan basuka.