Da sana’ar kifi yarana suka yi karatu har jami’a - Lilian
Da sana’ar kifi yarana suka yi karatu har jami’a - Lilian
An wallafa
Lilian Rikko, mai kiwon kifi a Abuja, babban birnin Najeriya ta ce ta soma sana’ar kifi ne da guda 30 amma yanzu sana’ar ta bunkasa sosai.
A cewarta da kiwon kifi take ciyar da kanta kuma ta sa yaranta a makaranta a yanzu inda wasu har sun kai matakin karatu a jami’a.
A cikin wannan bidiyon, Lillian Roko ta bai wa masu son sana’ar kifi shawarwarin da za su bi domin samun nasara a sana’ar.



