Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
David Silva ya yi ritaya daga taka leda
Tsohon dan kwallon Manchester City, David Silva ya sanar da cewar ya yi ritaya daga murza leda.
Mai shekara 37 dan kasar Sifaniya ya kwashe sama da shekara 10 a City da lashe Premier League hudu daga baya ya koma Real Sociedad a 2020.
Silva na fama da yawan jinya musamman a lokacin nan da ake atisayen tunkarar kakar da za a fara a cikin watan Agusta.
Dan kwallon ya kawo karshen shekara 19 da ya yi yana sa'ar taka leda.
Tsohon dan kwallon Sifaniya ya koma City daga Valencia a 2010, wanda ya yi karawa 436 da cin kwallo 77 a kungiyar ta Etihad.
Fitatcen dan kwallon City, an kaddamar da butum butuminsa a filin wasa na Etiha a 2021 tare da na Vincent Kompany da na Sergio Aguero.
Bayan kofunan Premier League da ya dauka a City, ya kuma lashe FA Cup biyu da League Cup biyar.
Silva ya yi ritaya daga yi wa Sifanya tamaula a 2018, bayan lashe kofin duniya a 2010 da na nahiyar Turai a 2008 da kuma 2012 wato European Championship.