Kama masu zanga-zanga a raka gawar Sarauniya ya sanya damuwa kan 'yancin fadin albarkacin baki

Asalin hoton, PA Media
Masu fafutukar fadin albarkacin baki sun ce ana cikin damuwa bayan kama wasu masu zanga-zanga bayan mutuwar Sarauniya Elizabeth II.
‘Yan sandan Scotland sun zargi wasu mutum biyu, tare da kama wani guda daya da sake shi a Oxford.
Kamen na zuwa ne a daidai lokacin da ake hidimomin jana'izar Sarauniyar ta Ingila da kuma ayyana ɗanta Charles a matsayin sabon Sarki na III na masarautar Birtaniya.
A birnin Landan, yayin da mutane ke shiga dogayen layuka domin ganin yadda ake wucewa da gawar sarauniyar, ‘yan sandan Met sun ce mutane na da hakkin yin zanga-zanga.
Ana zargin wani mai shekara 22 da hannu wajen tayar da zaune tsaye bayan da ya kawo hargitsi lokacin da Duke na York suka yi jerin gwano domin ganin gawar Sarauniyar Elizabeth a Edinburgh ranar Litinin.
Hotunan bidiyo da suka karade shafukan sada zumunta, sun nuna wani mutum yana yi wa Yarima Andrew ihu lokacin da yake jiran ganin gawar Sarauniyar, kafin wasu mutum biyu su janye shi daga wajen.
Hakan na zuwa ne bayan da aka zargi wata mata mai shekara 22 da laifin kawo hargitsi lokacin ayyana sabon Sarki Charles na III a Cocin St Giles, kwana guda kafin nan.
Dukkan mutanen dai an sake su, inda nan gaba za su bayyana gaban kotu a Edinburgh.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A duk dai ranar, an kama Symon Hill, mai shekara 45 da zargin tayar da husuma cikin jama’a bayan yin ihu da cewa ‘‘Wa ya zabe shi’’, a Oxford.
‘Yan sanda sun ce daga baya an sake shi, inda kuma yake taimaka wa jami’anta da wasu ayyuka.
Ruth Smeeth, shugabar kungiyar fafutukar ƴancin fadin albarkacin baki ta Index on Censorship, ta ce kamen abun damuwa ne matuka, inda ta kara da cewa ‘Dole ne mu kiyaye ka da a yi amfani da wannan taron, don tauye ‘yancin fadin albarkacin baki da ‘yan kasar nan ke mora.’’
Shi ma Silkie Carlo, daraktan kungiyar fafutuka ta Big Brother Watch, ta ce ‘yan sanda na da ‘alhakin kare hakkin mutane na yin zanga-zanga muddin suna da hakkin nuna goyon baya da yin jimami da kuma girmamawa.’’
Jodie Beck, jami‘ar tsare-tsare a wata kungiyar fararen hula, ya ce ‘’abun damuwa ne ganin yadda ‘yan sanda ke amfani da karfi fiye da ƙima kan mutane’’.
"Zanga-zanga ba dama ba ce ta kasa, sai dai hakki ne da dokar kasa ta bai wa mutane," in ji Jodie.

Asalin hoton, OTHER
A ranar Litinin, ‘yan sanda sun kori wani mai zanga-zanga da ke rike da wata alama da ke cewa ‘Ba Sarkina ba ne’’ a wajen majalisar dokoki gabanin isowar Sarkin a fadar Westminster Hall.
‘Yan sandan birnin Landan, sun ce an bukaci wani mutumi da ya bar fadar Westminster ‘domin bai wa ababen hawa wurin shiga’’ amma ba a kama ko kuma a ce masa ya bar fadar ba.
‘Yan sandan sun kuma mayar da martani kan wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, inda aka jiyo wani jami’in dan sanda na tambayar bayanan wani da ya rike wata takarda da ke cewa ‘Ba Sarkina ba ne’’.
Jami’in – wanda aka ruwaito cewa yana aiki ne da wata rundunar tsaro domin taimakawa ‘yan sandan na birnin Landan – an jiyo shi yana cewa sakon ‘’zai iya ɓata wa mutane rai’’.
Wata sanarwa daga mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Stuart Cundy, na cewa ‘Jama’a na da hakkin yin zanga-zanga, kuma muna nanata hakan ga dukkan jami’anmu da ke bakin aiki.’’
Sama da sojoji 1,500 ne za su yi aiki tare da ‘yan sanda da kuma masu kula da fararen hula domin aikin takaita dumbin mutane da ake saran za su shiga birnin Landan a mako mai zuwa.
Sabon kwamishinan ‘yan sandan birnin Landan, Sir Mark Rowley, ya ce jami’an na fuskantar gagarumin kalubale.
"Za mu gudanar da bikin lami lafiya, amma za mu girke dubban jami’ai saboda bukatar samar da tsaro ga miliyoyin mutane da ke son yi wa gawar Sarauniya girmamawa ta karshe,’’ a cewar Rowley.
Mai magana da yawun firaministan kasar bai ce komai ba kan kame da aka yi wa mutane, sai dai ya ce ‘Yanzu lokaci ne na zaman makoki na kasa baki daya.
''Amma ‘yancin yi zanga-zanga ya kasance babban ginshiki na dimokuradiyya.’’












