Chelsea ta dauki Wesley Fofana

An wallafa

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta kammala daukar dan wasan baya na Faransa Wesley Fofana daga Leicester City kan fam miliyan 70 kan kwantiragin shekara bakwai

Dan wasan mai shekara 21 ya koma Leicester City da ga kungiyar Saint-Etienne ta Faransa a shekarar 2020, inda ya buga wasan Premier 37, to sai dai wasannin Premier bakwai kawai ya samu bugawa a kakar wasa ta 2021 saboda karaya da ya samu a kafa a wasan da kungiyarsa ta kara da Villarreal a wasannin share fagen fara kakar wasa.

Dan wasan ya ce ''na ji dadin komawa Chelsea, ina cikin farin cikin fara wasa a kungiyar, na zo Chelsea ne domin samun nasarar daukar kofuna''

Kawo yanzu dai kungiyar Chelsea ta dauki 'yan wasa shida wadanda suka hadar da Raheem Sterling daga Manchester City, sai Kalidou Koulibaly daga Napoli da Carney Chukwuemeka daga Aston Aston Villa da Marc Cucurella daga Brighton, da kuma Cesare Casadei daga Inter Millan

A halin yanzu dai kungiyar na mataki na takwas a kan teburin Premier bayan da ta yi rashin nasara a hannun Southampton ranar Talata da ci 2-1