Madrid na yunƙurin ɗauko Bellingham Ronaldo na rikici da ejan kan makomar ƙwallonsa

An wallafa

Ɗan wasan tsakiyar Ingila da ke bugawa Borussia Dortmund Jude Bellingham, mai shekara 19, shi ne babban burin ƙungiyar Liverpool amma kuma suna shirin ɗaukar wani ɗan wasan tsakiyar daban wanda bai kai Jude fice ba a watan Janairu. (Football Insider)

Bayan kallon ƙwazonsa a Gasar Cin Kofin Duniya, Real Madrid a yanzu na jin cewa su ne "suka fi dacewa da shi" a yunƙurinsu na cimma wata yarjejeniya da Jude Bellingham lokacin zafi yayin da Liverpool ke daɗa matsawa don ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Benfica daga ƙasar Argentina wato Enzo Fernandez, mai shekara 21.

Ɗan wasan gaba na Manchester City daga ƙasar Norway Erling Haaland, mai shekara 22, a yanzu ba ya cikin jerin 'yan wasan da Real Madrid ke harin ɗauka nan gaba bayan sun samu amincewar ɗan wasan gaban Brazil Endrick, mai shekara 16, daga Palmeiras wanda zai je Madrid a 2024. 

Barcelona har yanzu ba ta yi wata tattaunawa da Lionel Messi game da komawar ɗan wasan gaban na Argentina mai shekara 35, zuwa ƙungiyar ba, bayan ƙarewar kwanturaginsa da Paris St-Germain a ƙarshen lokacin zafi. 

Ƙurar rikici na ci gaba da turnuƙewa tsakanin Cristiano Ronaldo, ɗan shekara 37, da ejan ɗinsa Jorge Mendes daidai lokacin da ake fama da rashin tabbas kan makomar ɗan wasan gaban na Portugal bayan ya bar Manchester United

Kocin ƙungiyar Al Nassr Rudi Garcia zai yi maraba idan ya samu damar aiki da Ronaldo bayan rahotannin cewa kulob ɗin na ƙasar Saudiyya na da sha'awar sa hannu kan yarjejeniya da shi, kocin ɗan ƙasar Sifaniya ya ce "ƙiris ya rage" bara ya gaji Ole Gunnar Solskjaer a matsayin kocin Manchester United

Ronaldo dai ba zai jingine takalmansa daga buga ƙwallon ƙafa na ƙasashen duniya ba bayan cire Portugal daga Gasar cin Kofin Duniya, ko da Fernando Santos ya ci gaba da kasancewa kocin ƙasar. (Correio da Manha - in Portuguese)

Kocin Roma Jose Mourinho yana kan gaba a jerin Portugal na masu son maye gurbin Santos a matsayin babban kocin ƙasar. 

Tottenham na da sha'awar ɗaukar Wilfried Zaha, mai shekara 30, a matsayin aro idan kwaturagin ɗan wasan gaban na ƙasar Ivory Coast ta ƙare a Crystal Palace lokacin zafi da ke tafe. 

Chelsea na shirin ɗauko wani sabon ɗan wasan gaba a watan Janairu kuma har sun fara tattaunawa kan yiwuwar haka tun ma kafin ɗan wasan gabansu na ƙasar Albania Armando Broja, mai shekara 21, ya ji mugun rauni a gwiwarsa. 

Manchester United har yanzu ba su bi sawun Chelsea ba don nuna sha'awa kamar dai AC Milan wajen ɗauko dan wasan gaban Portugal, Rafael Leao, mai shekara 23. 

Ɗan wasan baya Luizao ya sauka a Ingila don yin gwajin lafiya a kulob ɗin West Ham duk da yake ba shi kaɗai ne dan ƙwallon Brazil mai shekara 20 da suke fatan ɗauka daga Sao Paulo ba, tun da har ma sun fara tattaunawa don cimma wata kwangila da ɗan wasan tsakiya Pablo Maia. 

Barcelona na kallon ɗan wasan tsakiyar Argentina daga ƙungiyar Boca Juniors Alan Varela, mai shekara 21, a matsayin wanda mai yiwuwa ya maye gurbin daɗaɗɗen kaftin ɗinsu Sergio Busquets, ɗan shekara 34.