Netanyahu na gab da yin nasara a zaɓen Isra'ila

An wallafa

Tsohon Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na kan hanyar samun nasara a babban zaben kasar da aka gudanar, kamar yadda sakamakon ra'ayin wadanda suka kada kuri'a ya nuna.

Hasashen ya nuna cewa Mista Natenyahu na kan gaba da 'yar tazara a yawan kujerun da jam'iyyarsa za ta samu a majalisar dokokin kasar.

Wannan sakamako na hasashen dawowar Mista Netanyahu kan karagar mulkin da ya rasa iko da shi ne a shekarar da ta gabata bayan shafe shekara 12 a jere yana jagorantar kasar.

Netanyahu ya faɗa wa cincirindon magoya bayansa a birnin Kudus cewa ''muna dab da samun babban nasara''.

Da yawa dai na kallon zaɓen a matsayin zaben amincewa ko, adawa da dawowar mista Netanyahu kan karagar mulkin kasar.

Ra'ayoyin waɗanda suka kada kuri'a ya nuna cewa jam'iyyar mista Netanyahu za ta samu kujeru 61 ko 62 a majalisar dokokin kasar.

Anan gaba kadan ne dai a yau ake sa ran fara samun sakamakon farko na zaben.

Mista Netanyahu tare da matarsa Sara sun hallara a ofishin jam'iyyarsa cikin daren jira inda dubban magoya bayansu suka rika yi musu tafi da nuna murna.

''Mun samu gagarumin goyon baya daga al'umar Isra'ila,'' in ji Netanyahu a lokacin da yake yi wa taron magoya bayansa jawabi.

Tun lokacin da aka bayyana sakamakon ra'ayoyin wadanda suka jefa ƙuri'a sa'o'i kadan bayan kammala zaɓen, ofishin jam'iyyarsa ya cika da magoya bayansa cikin murna, inda suka yi ta tsalle tare da ɗaga tutocin jam'iyyar, sannan suka yi ta rera wakoki tare da kiran Bibi, wato lakabin Mista Netanyahu.

Mista Netanyahu mai shekara 73, na daya daga cikin 'yan siyasar kasar masu janyo ce-ce-ku-ce, wanda kuma ke samun gagarumin goyon bayan talakawan kasar.

Babban mai goyon bayan ci gaba da gine-ginen Israila a gabar yamma da kogin Jodan ne, wanda ta mamaye tun a shekarar 1967 a lokacin yakin gabas ta tsakiya.

Ana yi wa gine-ginen kallon wadanda suka sabawa dokokin kasashen duniya, to sai dai Isra'ila ta ki amincewa da hakan.

Yana matukar adawa da matakin - samar da kasar Falastinawa a gabar yamma da kogin Jodan da kuma yankin zirin gaza, a matsayin masalaha ga yaki tsakanin kasashen biyu - matakin da kasashen duniya da dama ke maraba da shi ciki har da gwamnatin Joe Biden na Amurka.

Mista Netanyahu dai na fuskantar shari'a kan zargin cin hanci, da zamba, da cin amana, zarge-zargen da ya sha musantawa.

Wadanda ake ganin za su zama abokan gwamnatin hadakarsa, sun ce za su kawo sauye-sauye a dokokin kasar, a wani yunkuri na soke shari'ar da ake yi masa.

Sakamakon ra'ayoyin wadanda suka kada kuri'a ya nuna cewa jam'iyyar Likud mai samun goyon bayan 'yan kishin kasa da kungiyoyin addinai, ka kara samun tagomashi, inda ake ganin za ta samu kujeru 30 zuwa 31 amajalisar dokokin kasar.

Yesh Atid - wanda jam'iyyarsa ta jagoranci gwamnatin hadakar da ta kawo karshen mulkin Netanyahu a shekarar da ta gabata - ana ganin jam'iyyarsa za ta samu kujeru 22 zuwa 24.