Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Darwin Nunez ya bai wa hammata iska da ƴan kallo
Ɗan wasan Liverpool Darwin Núñez ya samu saɓani da ƴan kallo bayan an kammala wasan da Uruguay ta sha kashi a hannun Colombia.
An ga ɗan wasan gaban yana tunkarar magoya bayan Colombia bayan an tashi wasan kusa da na ƙarshen na gasar Copa America.
Rahotanni sun bayyana cewa, rikici ya ɓarke a kusa da inda ƴan uwa da abokai na tawagar Uruguay ke zaune.
Núñez dai har yanzu bai ce uffan ba a kan lamarin.
An ɗauki hotunan Núñez yana afkawa cikin cunkoson jama'a a filin wasa na Bank of America da ke birnin Charlotte a jihar North Carolina.
An gan ga lokacin da ya ke fuskantar magoya bayan Colombia yayin da wasu ke ƙoƙarin hana shi.
An ruwaito cewa wasu ƴan wasan Uruguay ma sun shiga cikin lamarin.
Kyaftin ɗin Uruguay José María Giménez ya ce ƴan wasan na ƙoƙarin kare iyalansu ne.
Jim kaɗan kafin a fara rikici da ƴan kallon, ƴan wasa da masu horar da ƴan wasa sun yi arangama a filin wasa bayan kammala wasan.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Kudancin Amurka (Conmebol) ta yi allawadai da lamarin, ta kuma ce za ta gudanar da bincike cikin gaggawa.