Matashin da ya gagari cutar da ke cin ƙwaƙwalwa a Indiya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Imran Qureshi

BBC Hindi, Bengaluru

An danganta nasarar tsira da wani matashi ya yi daga wata cuta mai cin ƙwaƙwalwa da sanarwa ta faɗakar da jama'a da aka sanya a shafukan sada zumunta da muhawara.

Wannan ya sa matashi, Afnan Jasim mai shekara 14, ya zama mutum na tara a duk duniya da ya yi irin wannan sa'a.

Ana ganin Afnan ya kamu da ƙwayar cutar a watan Yuni bayan da ya je wanka a wani kududdufi a jihar Kerala da ke kudancin ƙasar.

Likitansa ya ce ƙwayar halittar (amoeba) da ke yi wa ƙwaƙwalwa wannan illa wadda ake kira Naegleria fowleri -kila ta shiga jikinsa ne a lokacin da yake wanka a wannan ruwa da ya gurɓata da ƙwayar.

Cutar (Primary Amoebic Meningoencephalitis (PAM)) tana kashe kashi 97 cikin ɗari na mutanen da take kamawa.

Alƙaluman hukumar yaƙi da cutuka ta Amurka sun nuna cewa tsakanin 1971 da 2023, mutum takwas ne kawai suka tsira daga wannan cuta a ƙasashe huɗu - Australia da Amurka da Mexico da kuma Pakistan.

A dukkanin mutanen da ta kama ana gano alamun cutar ne a tsakanin sa'a tara zuwa kwana biyar bayan kamuwa da ita, wanda hakan na da muhimmanci sosai wajen samun lafiyarsu.

Ƙwararru a harkar lafiya sun ce gano cutar da wuri da soma yi mata magani na taka muhimmiyar rawa wajen maganinta.

Alamun cutar (PAM) sun haɗa da ciwon kai da zazzaɓi da amai da rikicewar ciki a kagewar wuya da jiri da suma ko jiye-jiye da gani-gani.

Likitan da ya yi wa Afnan magani, Dakta Abdul Rauf, ya ce yawanci ana samun ƙwayar da ke haddasa wannan cuta a rafi ko kogi ko kududdufi da ruwan yake da ɗumi.

Likitan ya ce, “Kada mutane su faɗa ruwa - ninƙaya - wannan tabbas ita ce hanyar da ƙwayar cutar za ta shiga jiki. Idan ruwan ya gurɓata da ƙwayar cutar daga nan za ta shiga jikinka ta hanci.

Abin da ya fi dacewa shi ne mutum ya guji ruwan da yake gurɓatacce.

Hatta a tafkin ninƙaya a wurare na musamman kamar otal-otal, likitan yana shawartar mutane kada su bari ruwa ya kai wajen bakinsu.

Sanya maganin tsaftace ruwa abu ne da yake da kyau da muhimmanci in ji Dakta Rauf.

Wata maƙala ta bincike da aka wallafa a jihar Karnataka ta bayar da rahoton yadda hatta jarirai da kananan yara a ƙasar ta Indiya da wurare irin su Najeriya ke kamuwa da cutar daga ruwan wanka.

Tun 1965, an samu rahotan mutum wajen 400 da suka kamu da cutar (PAM) a faɗin duniya, amma har zuwa yanzu Indiya ta samu ƙasa da mutum 30.

Likitan ya ce, jihar Kerala, ta bayar da rahotan mutum ɗaya da ya kamu da cutar a 2018 da 2020 kuma wannan shekarar an samu kusan mutum biayr da suka kamu.

Afnan ya fara jin alamun cutar kwana biyar bayan ya je kududdufi wanka a lardin Kozhikode. Sai ya fara shiɗewa yana kuma ƙorafi ya yawan ciwon kai mai tsanani.

Iyayensa sun kai shi wajen likita amma ba wani sauƙi da ya ji.

To amma sai aka yi sa'a mahaifinsa MK Siddiqui, mai shekara 46, ya taɓa karanta alamun wata cuta da ya gani a shafukan sada zumunta da muhawara inda ya ga alamun cutar ɗan nasa ta yi kama da abubuwan da ya karanta.

Siddiqui, wanda mai kiwon shanu ne ya ce bayan da ya ga shiɗewar da Afnan ke yi ba ta tsaya ba sai ya kai shi wani asibitin daban.

To amma kuma babu likitan ƙwaƙwalwa a wannan asibitin.

A ƙarshe dai sun je asibitin Baby Memorial Hospital a Kozhikode, inda Dr Rauf, ƙwararren likitan yara yake.

Dr Rauf ya yaba da yadda Siddiqui ya yi wa likitoci bayani a kan wankan kududdufi da ɗansa ya je da kuma alamun cutar da ya gani, wanda wannan ya sa sun iya gano cutar da wuri.

Kafin a kai Afnan asibiti akwai mutum uku da suka rasu sakamakon kamuwa da cutar a jihar Kerala.

"Bayan wannan sai muka gaya wa gwamnati, saboda abu ne da ya shafi lafiyar jama'a, daga nan sai aka ƙaddamar da kamfe na faɗakar da mutane, in ji Dr Rauf.

Wannan faɗakarwa ita ce mahaifin yaron ya gani a shafukan intanet.

Likitoci sun yi gwaji a kan Afnan, wannan ya taimaka wa likitocin gano ƙwayar cutar a jikin yaron, inda daga nan aka fara yi masa magani.

Magungunan da ake amfani da su wajen jinyar cutar sun haɗa har da wani da babu shi a Indiya (Miltefosine), sai da aka siyo shi daga Jamus.

Yadda aka yi wa Afnan magani ya ji daɗi inda ya ce yana son ya yi digiri a aikin jinya.

"Ma'aikatan jinya suna ɗawainiya a kan marassa lafiya, ya gaya wa likitan," in ji mahaifinsa.