Bellingham zai buga wasan Ingila da Switzerland

Asalin hoton, Getty Images
Jude Bellingham zai iya bugawa Ingila wasan kusa da daf da na ƙarshe na gasar Euro 2024 da take gudana wanda za ta yi ranar Asabar.
Wannan na zuwa ne bayan dakatar da shi wasa guda tare da cin tararsa kan wata alama da ya nuna lokacin da yake murnan farke kwallon da aka ci su a wasan zagayen 'yan 16 da suka yi da Slovakia.
An jingine dakatarwar da aka yi masa sai nan da shekara kuma an ci tararsa fan 25,400 daidai da yuro 30,000.
Dan wasan tsakiyar ya kama gabansa ne a gaban 'yan wasan bencin Slovakia bayan farke kwallon da ya yi wanda daga baya Ingila ta yi nasara, abin da hukumar Uefa ta gudanar da bincike a kai kenan.
Bellingham wanda ya taba yin irin wannan murna a ƙungiyarsa ta Real Madrid, ya ce shi ba ya nufin ƙuntatawa abokan fafatawar Ingila da murnar.
Ya ce ba shi da wani abu ga 'yan wasan Slovakia bayan girmamawa.





