Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Mayar da Sarki Sanusi da bayar da belin Abba Kyari
An mayar da Muhammadu Sanusi II kan muƙamin sarkin Kano
A makon da ya wuce ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano.
Gwamnan ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan sanya hannu kan dokar da ta yi gyara ga dokar da ta kafa masarautun Kano guda biyar ta 2019.
A ranar Alhamis ne Majalisar dokokin ta jihar Kano ta soke ƙudurin dokar masarautu biyar na Kano - wato Kano, Bichi, Rano, Karaye da Gaya karatu na uku tare da amincewa da ita.
Daga nan ne aka miƙa dokar ga gwamnan wanda ya sanya mata hannu.
An kuɓutar da 'ya'yan ɗan majalisar Zamfara bayan wata 17 da sace su
A makon da ya gabata ne ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro tare da hadin gwiwar ƴan sanda suka ceto 'ya'ya mata biyu na wani ɗan majalisar jihar Zamfara da aka yi garkuwa da su watanni 17 da suka gabata.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa a ranar Talata ne aka miƙa yaran biyu, Maryam da Nana Asma'u ga mahaifin nasu Aminu Ardo a hedikwatar ƴan sanda ta ƙasa da ke birnin Abuja.
A lokacin miƙa wa ɗan majalisar 'ya'yan nasa, mataimakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, CSP Isuku Victor ya ce mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro Mallam Nuhu Ribaɗo ne ya jagoranci ƙoƙarin ceto yaran tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro.
A watan Nuwanbar 2022 ne ƴan bindiga suka kai hari gidan Aminu Ardo a Jangebe da ke jihar Zamfara tare da yin garkuwa da matarsa da kuma ƙananan yaransa huɗu.
NLC ta sake fatali da tayin N57,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi
Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC ta sake yin watsi da tayin naira 57,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasar da kwamitin ƙarin albashin ya yi mata.
Wannan ne karo na uku da NLC ke watsi da ƙarin da gwamnatin ta yi masa cikin kusan mako guda.
A ranar Talata ne NLC ta yi watsi da tayin naira 54,000 da gwamnatin ƙasar ta yi wa ma'aikatan ƙasar, bayan da a makon da ya gabata ƙungiyar ta ƙi amincewa da tayin naira 48,000 daga ɓangaren gwamnatin ƙasar.
Ƙungiyar dai ta bai wa gwamnatin ƙasar wa'adin zuwa ranar 31 ga watan Mayun da muke ciki domin cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashin.
Kotu ta bai wa Abba Kyari beli na mako biyu
A makon da ya gabata ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon mataimakin kwamishinan ƴan sanda a Najeriya DCP Abba Kyari na tsawon mako biyu.
Kotun ta ce ta bayar da belin nasa ne domin ba shi damar zuwa gida don ta'aziyyar mahaifiyarsa wadda ta rasu.
Kotun ta bayar da belin ne kan kuɗi naira miliyan 50 da kuma wani wanda zai tsaya masa.
Haka nan kotun ta ajiye ranar 31 ga watan Mayu domin sauraron takardar da Abba Kyarin ya shigar ta neman beli.
Yadda faɗuwar darajar naira ta sa aka kori ɗaliban Najeriya daga Birtaniya
A makon da ya wuce ne aka kori wasu ɗalibai ƴan Najeriya daga makaranta tare da ba su umarnin barin Birtaniya saboda gazawa wajen biyan kuɗin makaranta sakamakon faɗuwar darajar kuɗin ƙasar tasu naira.
Hakan dai ya faru ne a Jami'ar Teesside, wadda ta dakatar da ɗaliban daga shiga aji saboda rashin biyan kuɗin makaranta a kan lokaci.
Wasu daga cikin waɗanda lamarin ya shafa sun shaida wa BBC cewa, matakin Jami'ar ya sanya sun ji kamar su kashe kansu, inda suka zargi jami'ar da ɗaukar mataki na rashin tausayi.
Najeriya dai na fama da matsin tattalin arziƙi da faɗuwar darajar kuɗin ƙasar naira, lamarin da ya jefa da yawan ɗaliban ƙasar da ke karatu a Birtaniya cikin halin ha'ula'i.
Tsofaffin ƴan sanda na zanga-zanga a Abuja
Jami'an ƴan sandan Najeriya da suka yi ritaya, waɗanda ke karkashin tsarin fansho na karo-karo (contributory pension scheme), sun yi zanga-zanga a harabar majalisar dokokin ƙasar da ke Abuja a makon da ya gabata.
Tsofaffin jami'an da suka taru a harabar majalisar sun yi korafi ne a kan rashin biyansu kuɗinsu na fansho na tsawon watanni.
Tsofaffin ƴan sandan da ke wakiltar rassansu na jihohi daban-daban sun kokawa da irin wahalar da suke ciki a kan ƙin biyansu haƙƙin nasu da hukumar fansho ta ƙasar ta yi.
Haka kuma sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fitar da su daga cikin wannan tsari na fanshon karo-karo.