Matakai biyar da suka tauye 'yancin matan Afghanistan

Afghan women's rights

Asalin hoton, NAVA JAMSHIDI/BBC

    • Marubuci, Yogita Limaye
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar Afghanistan
  • An wallafa

"Za mu bari mata su yi karatu da kuma aiki daidai da tanadin dokokinmu. Mata za su shiga a dama da su sosai a cikin ayyukan al'ummarmu." Abin da ƙungiyar Taliban ta ce ke nan a jawabin da ta yi bayan ƙwace mulki a ranar 15 ga watan Agustan 2021.

Shekara biyu ke nan amma Taliban ta yi fatali da duk waɗannan tabbaci da ta bayar. Tauye 'yancin mata a gwamnatinsu ya yi ƙamari fiye da kowanne a fadin duniya, ga tsauraran dokokin addini da ta kawo da kuma wasu dokokin yanki da ake amfani da su a sassan Afghanistan.

A duk wannan lokaci, BBC tana shiga don tattaunawa da mata, inda suka riƙa yin bayanin irin tashin hankali da tsoro da fatan da suke da shi don kuwa rayuwarsu ta tagarraya.

Satumbar 2021 - Hana mata zuwa sakandare

Matakin farko da ke manuniya ga matsayar Taliban a kan mata ya bayyana ne wata ɗaya bayan sun karɓi gwamnati. Ma'aikatar ilimi ta iitar da sanarwar cewa an buɗe makarantun sakandare ga yara maza amma ba ta ce komai a kan mata ba.

"A yankunanmu, an shaida mana cewa kada mu je makaranta," wata ɗaliba ƴar shekara17 ta shaida wa BBC a birnin Kabul.

Ta ƙara da cewa: ''Tsawon shekara 11 na shiga yanayi mai hatsari a ƙoƙarin da nake yi na aiki tuƙuru don zama likita, na shiga mummunan hali.''

A cikin makon dai, magajin garin birnin Kabul ya umarci ma'aikatan gwamnati mata su yi zamansu a gida, baya ga waɗanda ke yin irin ayyukan da mata ne kaɗai za su iya yi.

Amma duk da haka akwai matan da ke da fatan abubuwa za su sauya. ''Sun bar jami'oi a buɗe, don haka ina fatan za su canza matakan nasu,'' inji wata ɗaliba.

Lokacin da muka ziyarci hedikwatar hukumar Hisba da Taliban ta kafa ƙarkashin ma'aikatar tabbatar da ɗa'a da kawar da alfasha, mun samu an kafa ta ne a cikin gini ɗaya da gwamnatin da ta gabata ta kafa ma'aikatar kula da harkokin mata, wadda Taliban ta rushe jim kaɗan bayan ta ƙwace madafan iko.

An faɗa mana cewa ana bari mata su shiga cikin ginin amma ba mu ga ko ɗaya da ta shiga ba.

"Ko me ya sa kuka rufe makarantun mata?" Tambayar da na yi wa kakakin Taliban, wanda ke cikin ginin da mayaƙan Taliban suka zagaye.

Sai ya kaɗa baki ya ce "ƴan matan ne da kansu ba su son zuwa makaranta,"

Da kuma na ƙalubalance shi sai ya ce: "Za mu buɗe makaratun ƴan mata a sassan ƙasar. Muna aiki ne don inganta tsaro."

Disamba 2021 zuwa Maris 2022 - Haramta yin tafiya da kuma karya alƙawari game da karatun sakandare

Kandahar girls' school in 2011 (top) and this week (bottom)

Asalin hoton, NAVA JAMSHIDI/BBC

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mata sun yi tattaki a biranen Afghanistan don nuna rashin amincewa da haramta masu zuwa makaranta. Kuma a lokuta da dama gwamnatin Taliban ta yi amfani da ƙarfin jami'an tsaro wajen hana su zanga-zangar.

Wata da ta shiga zanga-zangar da muka haɗu da ita a sirrance a gidan wata ƙawarta ta ce: "An naɗa mani duka da wayar wuta."

Tana ɓoyo ne daga wuri zuwa wuri don tsoron kada a kama ta.

A watan Janairun 2022, mata masu fafutukar 'ƴanci aƙalla hudu aka kulle. An tsare su na tsawon makonni, inda aka riƙa naɗa masu duka.

Gwamnati ta ci gaba da sanar da dokoki da ƙa'idoji game da rayuwar mata. A watan Disamban 2021 gwamnatin Taliban ta ce dole ne duk matar da za ta yi tafiyar da ta kai kilomita 72 ta samu rakiyar namiji muharraminta.

Kwatsam sai aka ji kamshin canjin alheri.

A ranar 21 ga watan Maris ɗin 2023, ma'aikatar ilimi ta Taliban ta sanar da cewa ''Dukkan ɗaliban ƙasar za su koma makaranta a sabon zangon karatu''.

Jami'an Taliban da dama sun faɗa mana cewa za a sake buɗe makarantun mata a ƙasar.

Kwana biyu bayan wannan sanarwa, wata tawagar BBC ta shaida yadda ɗalibai mata suka shiga makarantar Sayed ul Shuhada, inda suka riƙa share ƙurar da ke kan teburan karatunsu cikin murna bayan shiga aji. Sai dai yanayi ya canza cikin ƴan mintuna.

Wani jami'in Taliban na yankin ya aike wa shugaban makarantar saƙo ta manhajar WhatsApp, inda ya ce a ci gaba da rufe makarantun sakandare har sai baba ta gani.

Ɗalibai da dama sun fashe da kuka. Ɗaya daga cikinsu mai suna Fatima ta riƙa cewa ''Wace irin ƙasa ce wannan? Mene ne laifinmu?''

A gefe guda kuma malaman addini da jagororin al'umma da dama suna cikin waɗanda suka taimaka wajen ganin Taliban ta kafa gwamnati, yayin da kuma akwai tsoro daga ɓangaren gwamnati cewa za ta iya fuskantar tirjiya idan ta zartar da wani mataki da ya saɓa matsayar dattijan da ke goyon bayanta.

Mayun 2022 - Fitar da sabuwar ƙa'idar sanya tufafi

Kabul

Asalin hoton, NAVA JAMSHIDI/BBC

Ƙasa da wata biyu, a ranar 7 ga watan Mayun 2022, gwamnatin ta sanar da wata doka da ta samu amincewar babban jagoranta, Mullah Haibatullah Akhundzada, inda ta tilasta wa mata sanya tufafin da zai rufe jikinsu daga kai zuwa tafin ƙafa.

Dokar ta ce: "Dole ne matan da ba su tsufa ba su sanya tufafin da za su rufe jikinsu baki ɗaya, baya ga idanunsu da aka yarda su bari a buɗe."

Dokar ta kuma ce dole ne maza su tabbatar cewa mata daga iyalinsu sun yi biyayya ga dokar ko kuma su ma su fuskanci hukunci.

Mun gani da ido yadda aka samu raguwar mata a kan tituna, da kuma yadda waɗanda suka fito suke bayyana a rufe ruf.

Mata sun koma sanya baƙaƙen riguna dogaye, da hijabai da kuma takalma masu rufe ƙafa baki ɗaya.

Ɗaya daga cikin matan ta ce: "Ba mu damu da yadda suke so mu fito ba, indai za su bari mu yi karatu kuma mu yi aiki''.

An kuma samu ƙaruwar mata mabarata, saboda an hana wasu daga cikinsu zuwa aiki don samun kuɗin kula da ƴaƴan da ke gabansu.

Mun kuma riƙa samun rahoton ƙananan yara mata da aka yi wa auren wuri saboda suna zaune a gida babu makaranta.

Oktoba zuwa Disaman 2022 - Hana mata karatun jami'a da bayyana a taron jama'a da kuma haramta musu aikin ƙungiyoyi masu zaman kansu

Kabul

Asalin hoton, NAVA JAMSHIDI/BBC

A Oktoban 2022, an shafe watanni ba tare da ɓullowar sabuwar doka daga gwamnati ba.

Da suka bai wa mata damar rubuta jarabawar shiga jami'a sai murna da farin ciki ake don fatan komai zai tafi daidai.

A bayyane take ƙarara cewa akwai rabuwar kai tsakanin Taliban a game da batun ilimin mata.

Kakakin Taliban, Zabiullah Mujahid ya shaida mana cewa: "Wasu malaman addini ba su yarda da karatun mata ba. Gwamnati tana ƙoƙarin cimma matsaya ne don ɗaukar matakin da ya kamata a kai''

Amma manyan jagororin ƙungiyar da ke a Kandahar sun ci gaba da jaddada matsayarsu ta tauye 'yancin mata har zuwa ƙarshen shekara.

A cikin watan Nuwamba hukumar yaƙi da alfasha ta ƙasar ta shaida mana cewa an haramta wa mata shiga tashar mota ta birnin Kabul saboda rashin biyayya ga dokar Musulunci da aka same su da aikatawa..

An kuma saba ganin yanayin da za a kafa doka a wani gari amma daga baya ta karaɗe ƙasar baki ɗaya.

Wannan karon da muka ziyarci ma'aikatar, sai aka faɗa mana cewa mata ba su shiga amma an bari mun shiga saboda mu baƙi ne.

Wata ɗaliba ta ce: "Mu mata a Afghanistan, kowacce rana muna tashi da sabuwar doka da ta haramta mana wani abu.'' Ta ƙara da cewa ''na yi sa'a na kammala sakandare kafin zuwan Taliban. Amma ina tsoron za su iya hana mata karatun jami'a".

Ta kuwa yi gaskiya don a ranar 20 ga watan iDsamban 2022 ministan ilimi mai zurfi na Taliban ya sanar cewa an dakatar da zuwan mata jami'a a ƙasar.

Kwana huɗu bayan wannan sanarwa kuma aka ƙara fitar da wata mai zafin gaske, inda ma'aikatar bunƙasa tattalin arziki ta umarci ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki a Afghanistan su sallami matan da ke musu aiki ko kuma a kwace lasisinsu.

Yulin 2023 - Rufe wuraren gyaran gashi

Kabul

Asalin hoton, NAVA JAMSHIDI/BBC

Wuri na ƙarshe da mata za su iya taruwa ba tare da fuskantar hantara daga Taliban ba shi ne wurin gyaran gashi da kwalliyar mata.

Amma sanarwar da gwamnatin Taliban ta fitar a ranar 4 ga watan Yuli ta rufe waɗannan wurare ba ta zo da mamaki ga mafi yawan mutane ba.

An yi ƙiyasin cewa mata aƙalla 60,000 ne suke aiki a shagunan gyaran gashi a Afghanistan kafin sanar da wannan doka.

Ɗaya daga cikin masu shagon gyaran gashin ta ce: "Wannan ce kaɗai hanyar samun kuɗi ga iyalina. Mijina yana fama da rashin lafiya don haka ba zai iya zuwa aiki ba. Ta yaya zan ciyar da ƴaƴana yanzu?

Duk da hatsarin da ke tattare da hakan, ta ci gaba da yin gyaran gashi a gida saboda ta ce ba ta da wani zaɓi.

A cikin gidaje, mun gano cewa akwai mata da dama masu gudanar da ayyuka don neman na abinci, ciki har da makarantu da kuma gyaran gashi yayin da wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu ke ci gaba da ɗaukar mata aiki a sirrance.

An bai wa mata damar yin aiki a fannin tsaro da kiwon lafiya da kuma wasu ƙananan sana'oin hannu.

Haka kuma, lokaci zuwa lokaci ana samun matan Afghanisatn da ke fitowa kan titi don gangamin neman yanci, duk kuwa da hatsarin da ke tattare da hakan a ƙarƙashin gwamnatin Taliban.

Ɗaya daga cikin irin waɗannan mata ta shaida mana cewa: "Muna da bambanci da matan da Taliban ta murƙushe sheakara 20 baya. Mun canza, kuma dole su yi yarda da hakan, ko da kuwa za mu sadaukar da rayuwarmu ne a kan hakan."