Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saudi 2034: Saudiyya ta bayyana shirin gina filayen wasa 11
Saudiyya ta gabatar da shirin gina filayen wasanni 11 - ciki har da wanda aka shirya ginawa mai bisan mita 350 - a wani ɓangare na shirye-shiryen da ƙasar ke yi na karɓar baƙuncin gasar cin kofin duniya ta 2034.
Ana sa ran cewa filin wasan da ake shirin yi a birnin Neom, wanda birni ne da ba a ma gina shi ba a halin yanzu da ke yankin arewa maso yammacin ƙasar, zai karɓi baƙuncin wasan daf dana kusa da na ƙarshe guda ɗaya.
Saudiyya ba ta fuskanci wani hamayya a yunƙurinta na shirya gasar ba, kuma tana da wa'adin har zuwa watan Oktoba ta gabatar da shirye-shiryenta.
Daga cikin sabbin filayen wasannin 11, takwas za su kasance a Riyadh babban birnin ƙasar - ciki har da filin wasan Sarki Salman mai ɗaukan mutum 92,760, wanda zai karɓi baƙuncin wasan farko da na ƙarshe.
Biranen Jeddah da Al Khobar da Abha kuma za su karɓi baƙuncin wasu wasannin.
Gasar cin kofin duniya ta 2034, ita ce karon farko da za a gudanar da gasar da aka faɗaɗa a ƙasa guda.
Shirin na Saudiyya dai bai bayyana adadin kuɗaɗen da za a kashe wajen karɓar baƙuncin gasar ba, amma akwai yiwuwar tsare-tsaren da aka zayyana za su buƙaci ɗaruruwan biliyoyin daloli.
Hukumar ta Fifa za ta tabbatar da masu masaukin baƙin gasar a ranar 11 ga Disamban wannan shekarar.
Filayen da za su karɓi baƙuncin gasar
Riyadh
- King Salman International Stadium - Mai ɗaukan mutane 92,760
- King Fahad Sports City Stadium - Mai ɗaukan mutum 70,200
- Prince Mohammed bin Salman Stadium - Mai ɗaukan mutum 46,979
- New Murabba Stadium - Mai ɗaukan mutum 46,010
- Roshn Stadium - Mai ɗaukan mutum 46,000
- Prince Faisal bin Fahad Sports City Stadium - Mai ɗaukan mutum 46,865
- South Riyadh Stadium - Mai ɗaukan mutum 47,060
- King Saud University Stadium - Mai ɗaukan mutum 46,319
Jeddah
- King Abdullah Sports City Stadium - Mai ɗaukan mutum 58,432
- Qiddiya Coast Stadium - Mai ɗaukan mutum 46,096
- Jeddah Central Development Stadium - Mai ɗaukan mutum 45,794
- King Abdullah Economic City Stadium - Mai ɗaukan mutum 45,700
Al Khobar
- Aramco Stadium - Mai ɗaukan mutum 46,096
Abha
- King Khalid University Stadium - Mai ɗaukan mutum 45,428
Neom
- Neom Stadium - Mai ɗaukan mutum 46,010