Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An dakatar da Bellingham daga buga wasa biyu a La Liga
An dakatar da ɗan wasan Real Madrid, Jude Bellingham daga buga wasa biyu a La Liga, sakamakon jan katin da aka yi masa a wasan Osasuna.
Real Madrid ta tashi 1-1 a wasan mako na 24 da ta je gidan Osasuna ranar Asabar 15 ga watan Fabrairu.
An kori ɗan wasan tawagar Ingila a karawar a minti na 39, saboda faɗar kalaman da ba su da ce ba ga rafli, Jose Luis Munuera.
Kenan Bellingham ba zai yi wa Real Madrid wasan La Liga da za ta fafata da Girona da kuma Real Betis ba.
Tuni Real Madrid, wadda take ta biyu a teburin La Liga ta sanar cewar za ta ɗaukaka kara kan hukuncin.
Sai dai Bellingham zai buga wa Real Madrid sauran wasa har da karawa da Manchester City ranar Laraba a Champions League.
Real Madrid za ta kara da City a wasa na biyu na cike gurbi a gasar zakarun Turai a Santiago Bernabeu ranar Laraba, bayan da ta ci 3-2 a Etihad a makon jiya.
Real Madrid za ta fuskanci Real Sociedad a Copa del Rey nan gaba zagayen daf da karshe, kuma Bellingham zai iya buga fafatawar.
Ɗan ƙwallon mai shekara 21 zai koma buga wa Real Madrid karawar La Liga a wasa da Rayo Vallecano ranar 9 ga watan Maris.
Real mai rike da kofin La Liga na bara ta yi wasa uku baya ba tare da nasara ba a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Ranar Litinin Barcelona ta koma ta ɗaya a kan teburin La Liga da maki 51, iri ɗaya da na Real ta biyu da kuma Atletico ta uku mai maki 50.