Champions League: Halin da ƙungiyoyi ke ciki a wasannin karshe

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Za a kammala wasannin cikin rukuni a Champions League da za a yi wasa 18 tsakanin ƙungiya 36 ranar Laraba.

Kawo yanzu an yi wasa bakwa-bakwai a cikin rukuni a gasar ta zakarun Turai ta bana, wadda aka canja wa fasali.

Waɗanda suka kai zagayen gaba kai tsaye: Liverpool, Barcelona

Ƴan 24 da za ake sa ran za su samu gurbi: Arsenal, Inter Milan, Atletico Madrid, AC Milan, Atalanta, Bayer Leverkusen, Aston Villa, Monaco, Feyenoord, Lille, Brest, Borussia Dortmund, Bayern Munich, Real Madrid, Juventus, Celtic.

Waɗanda ba su da tabbas: PSV, Club Brugge, Benfica, PSG, Sporting, Stuttgart, Manchester City, Dinamo Zagreb, Shakhtar Donetsk.

Waɗanda suka yi ban kwana da wasannin bana: Bologna, Sparta Prague, Leipzig, Girona, Red Star Belgrade, Sturm Graz, Salzburg, Slovan Bratislava, Young Boys.

Ƙungiya takwas ɗin farko a teburi za su kai zagayen gaba kai tsaye, yayin da daga mataki na tara zuwa na 24 za su buga karawar cike gurbi gida da waje.

Daga nan a samu 16 da za su ci gaba da wasannin zagayen kwata fainals a babbar gasar zakarun Turai ta bana.

Ranar Juma'a 31 ga watan Janairu za a raba jadawalin wasannin cike gurbi a Nyon.