'Maɗinkan Zariya masu fito da kwarjinin shigar Bahaushe'

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
'Maɗinkan Zariya masu fito da kwarjinin shigar Bahaushe'
An wallafa

Shigar Bahaushe tana ƙara samun tagomashi da karɓuwa a idon duniya, duk da tasirin zamani, hakan dai ba ya rasa nasaba da ƙoƙarin teloli.

Zariya na cikin mashahuran biranen ƙasar Hausa da ya yi fice da ɗinke-dinken hannu da sarakuna da masu faɗa-a-ji da kuma sauran al'ummar Hausawa suka dogara da su wajen fita kunya.

Matasa da dama na ƙara shiga sana'ar ɗinki tare da kawo sabbin dabaru da samfuran zamani cikin harkar.

Nau'o'in ɗinkunan zamani daban-daban sun sa tufafin Bahaushe na ƙara karɓuwa a tsakanin manyan mutane da jami'an gwamnati da jiga-jigan 'yan siyasa a ƙasashen Afirka ta Yamma kamar Nijeriya.