Arsenal ta shirya biyan kuɗin Nico Williams, Tottenham na neman Dibling

Asalin hoton, Getty Images
Tottenham na ƙoƙarin samo nagartattun masu kai farmaki, ciki har da Tyler Dibling na Southampton, Arsenal na ganin haske a ƙoƙarinta na ɗaukar yaron da ake ganin tauraruwarsa za ta haska nan gaba kaɗan, Sverre Nypan.
Tottenham ta tattauna da Soutahmpton a ƙoƙarin ɗaukar ɗan wasan tsakiya ɗan asalin Ingila Tyler Dibling mai shekara 18, da kuma ɗan wasan tsakiya Lille, ɗan asalin Ingila, Angel Gomes mai shekara 24. (Telegraph - subscription required)
Tottenham da Arsenal duk sun yarda su biya Yuro miliyan 58 domin ɗaukar ɗan wasan gefe na Athletico Bilbao da Spain, Nico Williams. (Fichajes - in Spanish)
Arsenal na kan gaba a ƙoƙarin sayen ɗan wasan tsakiya na Rosenborg da Norway, Sverre Nypan mai shekara 18. (Independent)
Bayer Leverkusen sun tuntuɓi Manchester City domin neman aron ɗan wasa James McTee ɗan asalin Ingila mai shekara 21 a duniya. (Daily Mail)
Da alama Pep Guardiola ba zai kawo wa ɗan wasan wata matsala ba idan har yana son tafiya. (Football Insider)
Aston Villa ta cimma yarjejeniya da ɗan wasan baya na Chelsea da France, Axel Disasi mai shekara 26. (Fabrizio Romano)
Haka nan ma Joao Felix mai shekara 25 na Chelsea na cikin ƴan wasan da ke ɗaukar hankalin Aston Villa, to amma ɗan wasa ɗaya ne kawai za su iya ɗauka aro daga Stanford Bridge. (Talksport)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ɗan wasan Aston Villa ɗan asalin ƙasar Colombia, Jhon Duran mai shekara 21 na daga cikin ƴan wasan da kulob ɗin Al-Nassr ke nema domin haɗa shi a gabansu tare da Cristiano Ronaldo. (Football Transfers)
Liverpool da Chelsea na son yin gogayya da Napoli a ƙoƙarin ɗaukar Karim Adeyemi mai shekara 23 na Borossia Dortmund da Jamus, amma wata kila dole su jira har zuwa lokaci na gaba da za a buɗe kasuwar musayar ƴan wasa. (Corriere Dello Sport - in Italian)
Real Madrid da Bayern Munich da kuma Jueventus na neman ɗan wasan baya na Bournemouth da Spain, Dean Huijsen mai shekara 21. (Fichajes - in Spanish)
Akwai yiwuwar Manchester United za ta ɗauki aron ɗan wasan gaba na Faransa, Christopher Nkunku mai shekara 27 daga Chelsea idan har Marcus Rashford mai shekara 27 ya bar ƙungiyar ta Manchester. (The Athletic - subscription required)
Rashford na ganin zai iya jira har sai ya samu damar tafiya Barcelona. (Mirror)
Chelsea na tunanin neman ɗan wasan gaba na RB Leipzig da Slovenia, Benjamin Sesko mai shekara 21, da kuma ɗan wasan gaba na Faransa da Bayen Munich Mathys Tel mai shekara 19, bayan da ƙungiyar ta fahimci cewa tana buƙatar ƙara wa gabanta ƙarfi a maimakon baya a wannan wata na Janairu. (TeamTalk)











