Ko Real Madrid za ta ci gaba da jan zarenta a kakar bana?

    • Marubuci, Ibrahim Mohammed Yusuf
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Zakarun gasar La Liga da na Turai Real Madrid na shirye-shiryen fara kakar wasa ta bana tare da sabon gogaggen ɗan wasa cikin jerin sunayen ƴan wasansu bayan da suka ƙara Kylian Mbappé a cikin tawagar Carlo Ancelotti.

Madrid za ta nemi maimaita nasarar da ta samu a kakar wasan da ta gabata inda ƙungiyar ta lashe gasar La Liga da kuma Champions League.

Kuma ƙungiyar ta fara shirye-shiryen da kafar dama bayan ta yi nasara kan Atalanta da ci 2-0, inda ta lashe kofin Uefa super cup ranar Larabar da ta gabata, kuma Mbappe ya ci wa ƙungiyar ƙwallonsa na farko.

Tuni dai aka cika filin wasa na Santiago Bernabéu maƙil don gabatar da ƴan wasa biyu a wannan bazarar, yayin da ƙungiyar ta tafi Amurka don fafatawa a wasannin sada zumunta inda ta sha kashi a hannun AC Milan a Chicago da kuma Barcelona a New Jersey, sannan kuma ta yi nasara a kan Chelsea a Charlotte.

Bayan nasarorin da ƙungiyar ta samu a kakar wasan da ta gabata mafi yawan masu sharhi kan al'amuran wasanni za su sa ido su ga ko ƙungiyar za ta iya ƙara taka rawar da ta yi a bara.

Shehu Abdullahi shi ne shugaban ƙungiyar marubuta labaran wasanni reshen jihar Kaduna kuma ya yi tsokacin cewa bisa ga dukkan alamu tawagar Real madrid ta bana ta fi ta bara ƙarfi sakamakon samun ɗan wasa ƙylliain Mbappe.

Ya ce: ''Wasan Uefa Super cup da Madrid ta buga ya nuna cewa ta ɗauko zaratan ƴan wasa a bana. A kakar wasan da ta gabata ƴan wasan ƙungiyar sun nuna bajintarsu inda suka lashe manyan gasa biyu kuma yanzu da ta ɗauko shahararren ɗan wasan duniya Mbappe, babu shakka ƙungiyar ta ƙara ƙarfi kuma zai yi wuya ba ta maimaita bajintar bara ba.''

Yadda ake ganin gasar La liga za ta kasance a bana

Real Madrid ta ƙara wa tawagarta ƙarfi da ƴan wasa biyu a wannan bazarar bayan ta kammala ɗaukar Kyllian Mbappé daga Paris Saint-Germain da kuma Endrick Felipe daga Palmeiras.

Mafi girman rashin da ƙungiyar ta yi daga kakar wasan da ta gabata ita ce murabus ɗin ɗan wasan tsakiya Toni Kroos.

Bajamushen ya rataye takalman wasansa ya kuma bar Ancelotti da babban giɓi a tsakiya. Haka kuma kyaftin Nacho, wanda ya bar kulob ɗin zuwa Al-Qadisiyah, sai kuma ɗan wasan gaba Joselu, wanda ya koma ƙungiyar Al-Gharafa ta ƙasar Qatar.

Ganin yadda sauran ƙungoyoyin La Liga ke shirin tunkarar kakar wasan bana, ba abin mamaki ba ne idan masu sharhi suka yi hasashen cewa Madrid ba za ta sha wahala wurin kai bantenta ba.

Barcelona - wadda ita ce babbar abokiyar hamayyar Madrid - na da alamun rauni ganin yadda ta shiga ruɗani a kasuwar cinikin ƴan wasa na bazarar nan, inda ya zuwa yanzu take kai wa da kawowa wurin neman ƴan wasan da za ta ɗauko domin ƙara wa tawagarta ƙarfi.

A yanzu ɗan wasa mai armashi ɗaya tilo da Barca da ɗauka shi ne Dani Olmo.

Ita kuwa Atlético Madrid ta yi manyan sauye-sauye a tawagarta inda ta sallami Alvaro Morata ta kuma maye gurbinsa da Julian Alvarez daga manchester City.

Ita kuma Girona da ta samu tagomashi a bara ta sallami ƴan wasanta da dama da suka taka mata rawar gani a kakar wasan.

Shehu Abdullahi ya ƙara da cewa: ''Al'ada ce ta La liga inda ƙungiyoyi uku ne ke fafutukar lashe gasar a kowace kaka, idan ka cire Real Madrid da Barcelona sai kuma Athletico Madrid, kuma a halin da ake ciki yanzu duk Madrid ta fi su ƙarfi, gami da cewa Carlo Ancelotti gogaggen koci ne wanda ya daɗe yana taka rawar gani a gasa daban-daban a Turai.''

A Turai, gasar za ta sake yin tsauri kamar yadda aka saba, amma Carlo Ancelotti ƙwararre ne a gasar zakarun Turai kuma zuwan Mbappe zai ƙara wa ƙungiyar ƙwarin gwiwa inda shi ma zai yi harin lashe kambunsa na farko a gasar, wanda kuma zai kasance wa ƙungiyar karo na uku cikin shekaru huɗu.

''Babu kocin da ya kai Ancelotti samun nasara a Champions League, kuma a kowace ƙungiya yake ana ganin yiwuwar zai iya lashe gasar, saboda haka ba za a yi mamaki idan Madrid ta sake yin nasara ba duk da cewa akwai ƙungiyoyi irin su Man City da ke tasowa yanzu kuma za ta iya gogayya da madrid a turai,'' In ji Abdullahi.

Yadda tawagar Madrid za ta iya kasancewa a kakar wasan 24/25

A ɓangaren mai tsaron gida, Thibaut Courtois ya taka rawar gani a wasannin share fage na wannan bazarar.

Duk da ƙoƙarin da Andriy Lunin ya yi a bara, ana sa ran ɗan wasan na Belgium zai kasance zaɓin farko na Carlo Ancelotti.

A masu tsaron baya, tafiyar Nacho na nufin cewa Éder Militão na shirin komawa matsayinsa na mai tsaron baya na tsakiya tare da Antonio Rüdiger.

A tsakiyar fili, ritayarToni Kroos ta bar babban giɓi. Mai yiwuwa wanda zai ci gajiyar hakan shi ne Eduardo Camavinga, wanda ya samu damar buga wasanni da dama a kakar wasan da ta gabata, kodayake Luka Modrić shi ma zai taka muhimmiyar rawa sakamakon gogewar da yake da ita wanda zai taimaka matuƙa a wasu wasanni.

A fannin ƴan wasan gaba kuma, zuwan Kylian Mbappé na nufin cewa dole ya ba a san yadda za a yi a yi wa Bafaranshen gurbi.

Ɗan wasan da ake ganin zai iya komawa benci shi ne ɗan wasan Brazil Rodrygo Goes, idan aka yi duba da irin hazakar Vinícius Júnior da Jude Bellingham.

Ana ci gaba da hasashe kan kasuwancin da ƙungiyar za ta iya yi a bazarar nan wanda ya shafi ɓangaren tsaron baya.

Ana alaƙanta mai tsaron raga Andriy Lunin da ficewa don neman gurbin buga wasa a wata ƙungiya, wanda hakan ka iya buɗe kofa ga yuwuwar dawowar ɗan wasan aro na bara, Kepa Arrizabalaga.

Bugu da ƙari, wasu masu sharhi na ganin cewa Los Blancos na buƙatar ƙarin ƙarfafa tsaron baya idan aka yi la’akari da labarin cewa David Alaba ba zai koma taka leda ba sai shekara mai zuwa.

Tun bayan rashin Lenny Yoro, wanda ya zaɓi komawa Manchester United, ɗaya daga cikin sunayen da aka ambata shi ne ɗan ƙasar Sifaniya Aymeric Laporte.

Ƴan wasa 11 na farko na 2024/25: Thibaut Courtois; Dani Carvajal, Éder Militão, Antonio Rüdiger, Ferland Mendy; Aurélien Tchouameni, Fede Valverde, Eduardo Camavinga; Jude Bellingham, Vinícius Júnior, Kylian Mbappé.