Ƙungiyar 'yan wasa na barazanar kai Fifa kotu kan gasar Kofin Duniya ta Kulob

An wallafa

Ƙungiyar 'yan wasan ƙwallon ƙafa ta duniya Fifpro ta yi barazanar maka hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa a gaban kotu idan ba ta janye shirinta na gudanar da gasar Kofin Duniya ta Kulob mai tawaga 32 ba.

Sun ce jadawalin Fifa "ya cika maƙil" har ma "gasannin wasu ƙasashe ba su iya tsara yadda za su gudanar da wasanninsu yadda ya dace", yayin da su kuma "'yan wasa ake takura musu da barazanar jin raunuka da rashin walwala".

Sashen BBC Sport ya ruwaito a Disamba cewa PFA na duba yiwuwar matakin shari'a game da cunkushewar jadawalin wasanni da kuma yadda hakan zai shafi mambobinta.

A kakar baɗi, za a mayar da dukkan gasannin zakarun Turai masu tawaga 32. Champions da Europa League za su fara da wasa takwas a zagayen farko idan aka kwatanta da shida da ake yi yanzu. Akwai yiwuwar sai kulob ya buga wasa 17 kafin ya iya lashe kofin gasar.

Manchester City da Chelsea na cikin ƙungiyoyin da za su buga gasar da aka faɗaɗa, wadda za a yi a Amurka a watan Yuni da Yulin shekara mai zuwa.

Cikin wata wasiƙa da suka rubuta wa shugaban Fifa Gianni Infantino da kuma babban sakatare Mattias Grafstrom, wadda BBC Sport ya gani, Fifpro da kuma ƙungiyar lig-lig ta duniya sun ce idan Fifa ta faɗaɗa gasanninta to ya kamata ta sauya wasu.

Ta ƙara da cewa "tilasta wa lig-lig da kuma 'yan wasa karɓar sauyin cin-zarafi babba" kuma "yana lalata lig na ƙasashe da shafar lafiya da walwalar 'yan wasa".

Sai dai BBC Sport ya fahimci cewa Fifa na ganin ta lura da walwalar 'yan wasan kafin ta sauya jadawalin gasannin.

Ta ce ƙungiyar lig-lig ta nahiyar Turai mai ƙarfin faɗa-a-ji ta amince da tsare-tsaren Gasar Kofin Duniya ta Kulob ɗin cikin wata sanarwa a watan Disamba.