'Onana ne gola na biyu mafi bajinta a Premier a bana'

An wallafa

Kocin Mnachester United Erik ten Hag ya ce golan ƙungiyar Andre Onana shi ne na biyu a masu tsaron ragar Premier “idan aka duba alƙaluman bajinta”.

Onana mai shekara 27 shi ne ya yi kura-kurai aka ci United kwallo biyu a wasan da ta tashi 3-3 da Galatasary wanda ya sanya har yanzu ƙungiyar ba ta son makomarta ba a Champions.

Bugu da ƙari golan na Kamaru shi ne ya fi buga wasannin da ba a zura masa ƙwallo ba, inda ya buga biyar ba tare da an zura masa ƙwallo ba.

Aƙaluman sun nuna cewa Onana na tare ƙwallo 3.67 da ya kamata su shiga ragarsa a kowane wasa, kuma shi ne mutum na biyu da ya fi wannan bajintar.

Mai tsaron ragar Luton Town Thomas Kaminski ne kawai gaba da shi, inda yake tare ƙwallo 6.3, a duk wasa.

Shafin Opta mai kawo ƙididdigar wasanni ne ya fitar da alƙaluman, bayan zare ƙwallayen da aka ci mai tsaron raga daga cikin adadin hare-haren da suka nufi raga da aka kai masa.

Da yake kare mai tsaron ragar nasa, Ten Hag ya ce: “Idan ka duba alƙaluman da kyau za ka tarar shi ne gola na biyu mafi ƙoƙari a Premier bana.”

A bana ne United ta sayi Onana kan kuɗi fan miliyan 47.2 daga Inter Milan, inda ya maye gurbin matsaron raga Devid de Gea, wanda kwantaraginsa ta ƙare a ƙungiyar a bana.

Bayan kuskuren da ya yi a Turkiyya, ya tafka wasu kura-kurai da ya sa United ta yi rashin nasara a Bayern Muncih da ci 4-3 a wasan farko na rukuni a Champions.

Ten Hag wanda ƙungiyarsa za ta fafata da Newcastle wannan Asabar ɗin da yamma, ya ce Onana: “yana ƙoƙari sosai.

''Ya kuma sani cewa a gasar Zakarun Turai yana kura-kurai, amma idan aka duba watanni biyar ɗinsa na farko za a ga ya yi ƙoƙari'', in ji Ten Hag.

“Kuma kana ganin yadda abin yake ɓata masa rai idan bai yi ƙoƙari ba, kamar yadda aka gani a Munich. Amma kuma a Burnley ya yi ƙoƙari.

“Dan wasa ne mai ƙwarin gwiwa, yana da ‘yan gyararraki da zai magance.”