Wasan ninƙaya a cikin hotunan Afirka

,

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Tsananin yanayin zafi a Masar ya sanya matasa wasan ninƙaya a kogi.
An wallafa
,

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mawaƙiya ƴar Najeriya, Ayra Starr, ke nan take rera sabuwar waƙar da ta fitar yayin gasar mawaƙa ta Montreux Jazz Festival wacce aka gudanar a Switzerland.
,

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Berihu Aregawi ya ɗaga kansa sama bayan ya kammala gudun mita dubu biyar a gasar wasanni ta Switzerland ranar Juma`a.
,

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mata sun rufe fuskokinsu saboda zafin rana a lokacin bukukuwan al`ada na Ojude Oba a ranar Juma`a.
,

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Dubban mutane sun halarci bikin na bana a Jihar Ogun.
,

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Hawan doki wani bangare ne na bikin na al`adun gargajiya.
,

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yaro ya na kallon yankin da gwamnati ta hana kamun kifi a tekun Ivory coast.
,

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ana gudanar da gasar wanda ya fi iya kwalliya yayin gasar tseren doki a Afirka ta Kudu.