Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An yi butun-butumin Vinicius Jr na cin zarafi da wariya
La Liga ta yi kakkausan suka kan yadda ake nuna tsana da cin zarafin dan wasan Real Madrid, Vinicius Junior.
Hakan ya biyo bayan wani butun-butumin dan wasan da aka yi na cin mutunci, wanda aka rataye a kusa da wata gada daf da filin atisayen kungiyar.
An kuma yi rubutu a wani kyalle cewar ''Birnin Madrid ya tsani Real, wanda aka saka a jikin gadar.
Atletico Madrid da Real za su fafata a Copa del Rey ranar Alhamis wasan quarter finals, sai dai Atletico ta ce ''wannan abin tir ne da aka aikata''.
Vinicius Jr dan kwallon tawagar Brazil, mai shekara 22 ya fada a baya cewar ya kamata mahukuntan La Liiga su dauki mataki kan wariya su kuma kawo karshen hakan.
Kafin wasan na hamayya tsakanin kungiyoyin Madrid a watan Satumba, wasu magoya bayan Atletico sun rera wakar cin zarafin Vinicius Jr.
Sun kuma yi hakan a filin wasa na Wanda Metropolitano lokacin da za a shiga fili a karawar da Real ta yi nasara da ci 2-1.
Masu shigar da kara a Sifaniya sun ce sun kammala bincike kan wadanda suka yi wa dan wasan kalaman cin zarafi, inda suka ce da wuya a fitar da wadanda suka aikata lafin.
A farkon watan nan mahukuntan La Liga sun ce sun shigar da tuhume-tuhume da ya shafi cin zarafin dan kwallon Brazil din ga kotuna da mahukuntan.
Ranar Alhamis La Liga ta ce za tsaurara bincike kan wadanda suka yi butun-butumin cin mutuncin Vinicius, domin ganin an hukunta su.