Ba na jin kunyar haɗa sana'ar gwanjo da waƙa - Ali Fiya Fiya
Ba na jin kunyar haɗa sana'ar gwanjo da waƙa - Ali Fiya Fiya
An wallafa
Matashin mawaƙi Ali Ussaini - wanda aka fi sani da Ali Fiya Fiya mai korona - ya ce ba ya jin kunya idan masoyansa suka gan shi a wurin sana'arsa ta sayar da kayan gwanjo.
Matashin ya ce ya fara waƙa tun a shekarar 2011 da waƙarsa mai suna "Fiya Fiya", inda ya samo sunansa ke nan.
"Tun ina fitowa ana gani na ana yi min dariya, har na saba da mutane," in ji shi game da kallon da mutane ke yi masa a wurin sana'arsa ta sayar da kayan gwanjo.
Kazalika, ya bayyana dalilin da ya sa ya yi waƙar "Mai Korona".



