To ko Barcelona ta hau turbar lashe La Liga na bana ne?

An wallafa

Barcelona ta ci gaba da jan ragamar teburin La Liga ta bai wa Real Madrid tazarar maki takwas karo na biyu a kakar nan.

Barcelona ta doke Sevilla 3-0 a wasan mako na 20 da suka kara a Nou Camp ranar Lahadi.

Hakan ya sa kungiyar da Xavi ke jan ragama ta hada maki 53 ta ci gaba da zama a matakin farko, ita kuwa Real ta biyu tana da maki 45.

A wasan da aka buga na mako na 20, Barcelona ce ta hada maki uku a tsakanin kungiyoyi shidan teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Cikinsu Atletico ce ta tashi 1-1 da Getafe ranar Asabar, Celta Vigo ta je ta doke Real Betis 4-3 ranar Lahadi.

A ranar Lahadin Real ta yi rashin nasara 1-0 a gidan Mallorca da wanda Valladolid ta je ta ci Sociedad 1-0 a karshen mako.

Barcelona ta ci kwallo ukun ta hannun Jordi Alba da Gavi da kuma Raphinha a wasan da ta yi a Nou Camp.

Kawo yanzu saura wasa 18 kenan maki 54 suka rage a karkare wasannin babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta bana.

Da yake Barcelona ta bai wa Real Madrid tazarar maki takwas, ko a iya cewa watakila kungiyar Camp Nou na turbar daular La Liga na kakar nan.

A tarihin gasar ta La Liga, duk kungiyar da ta bayar da tazarar maki takwas ko fiye da haka, bayan buga wasa 20 ita ce kan lashe kofin shekarar.

Karo takwas a baya da Barcelona ta ja ragamar teburin La Liga, bayan wasa 20 ta kuma bai wa Real Madrid tazarar maki takwas ko fiye da hakan, ita ce ta lashe kofin.

Ga jerin kakar da Barcelona ta yi wannan bajintar

1997/98, 1998/99, 2004/05, 2005/06, 2008/09, 2010/11, 2012/13, 2015/16, 2017/18 da kuma 2018/19.

To sai dai alkaluma kan iya canjawa a kowanne lokaci, kuma komai zai iya faruwa a fannin taka leda, musamman a kokarin lashe kofin 2022/23.