Tseren kwale-kwale da duba lafiyar dabbobi a hotunan Afirka na mako

Senegal

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Asabar, mutane na murna bayan an ƙaddamar da kwale-kwalen tawagarsu, a fara wasan tseren ruwa da ake yi a birnin Louis da ke gabatar teku a Senegal...
An wallafa
Senegal

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Dubban mutane sun halarci bikin, ciki har da mata kamar na hoton nan, waɗanda suke rera waƙoƙin tsuma waɗanda suka shiga gasar tseren ruwan....
Senegal

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An yi amanna da cewa sama da shekara 200 da suka gabata aka fara wasan, inda mutanen garuruwa da ƙauyuka ke halarta.
Rwanda

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Rwanda, wani mai wasanni ya sanya riga mai launi da zanen jikin rakumin dawa, a wata kasuwa da ke ci ranar Juma'a a Kigalia. Lokacin aikin hadin gwiwa tsakanin 'yan wasan dabe na kasar da Burundi da Belgium.
Tunusia

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mawakiyar Tunusia Noor Arjoun lokacin da take waƙa lokacin baje kolin mawaka a kasar ranar Laraba.
Kenya

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Litinin a birnin Nairobi na kasar Kenya, wata mace dauke da bokitin ruwa ta wuce kusa da bangon da aka lika hotunan dan takarar shugaban kasa Raila Odinga.
Kenya

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, An ci gaba da yakin neman zabe a Kangari, wani mai sayar da kayan miya ya zauna tsakiyar kayan da yake saidawa, ga kuma hotunan mataimakin shugaban ƙasa William Ruto, kuma dan takarar shugaban kasa a zaben watan gobe.
Afirka ta Kudu

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Talata a birnin Cape Town da ke Afirka ta Kudu, likitan dabbobi na duba lafiyar wani kare a asibitin dabbobi na Mdzananda.
Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wanshekare a dai birnin Cape Town, gungun mata sun taru a wajen kotu domin zanga-zangar kan rashin cika alkawarin gyaran wasu gidaje a yankin da ake yi wa lakabi da shalkwatar Afirka a Amazon.
Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Magoya bayan kungiyar kwallon kafar mata ta Banyana Banyana, a Afirka ta Kudu, lokacin da suka dawo gida daga kasar Moroko bayan yin nasarar daukar kofin nahiyar Afirka ta mata na 2022, an yi musu kyakkyawar tarba a birnin Pretoria inda za su gana da shugaban kasa.
Najeriya

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, 'Yar wasan Najeriya Tobi Amusan, ta na murnar kafa tarihi lokacin gasar tsere ta duniya a tseren mita 100 a wasan kusa da na karshe....
Najeriya

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Anan hoton ta ne dauke da allon kyautar dala dubu dari da aka bata da kambun zinare a wasan karshe na Oregon.
Uganda

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Juma'a a Uganda, mai fafutukar kare muhalli Patience Nabukalu, ta hade hannunta an dauki hoton a taron da aka yi na sauyin yanayi a duniya ranar Talata a kasar Italiya.
Cape Verde

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaban kasar Cape Verde, José Maria Neves, tlokacin taron manema labarai, bayan ganawa da takwaransa na Portugal a birnin Lisbon, ranar Alhamis.
Algeriya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Nau'uka da launi daban-daban na lamurje da aka hada musamman saboda masu halartar bikin baje kolin nau'o'in lemuka da kayan kwalam a babban birnin kasar Algeriya, Algiers, a ranar Juma'a.