Arsenal da Tottenham sun raba maki a wasan hamayya a Premier

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Arsenal da Tottenham sun tashi 2-2 a wasan mako na shida a gasar Premier League karawar hamayya ta kungiyoyin Arewacin Landan ranar Lahadi.

Arsenal ce ta fara cin kwallo ta hannun Cristian Romero, wanda ya ci gida a minti na 26 da take leda a Emirates, amma sauran minti uku hutu Heung-min Son ya farke.

Daga baya ne Gunners ta kara na biyu ta hannun Bukayo Saka a bugun fenariti, bayan da Romero ya taɓa kwallo da hannu a da'ira ta 18.

Kenan Romaro ya zama ɗan wasa na 11 a Premier League da ya ci gida ya kuma jawo bugun fenariti, kuma shi ne na farko a Tottenham.

Minti ɗaya tsakani da Arsenal ta ci kwallo, Tottenham ta farke ta hannun Heung-min Son, hakan ya sa sun raba maki a tsakaninsu a wasan hamayya.

Har yanzu ba a doke Gunners ba da fara kakar bana a Premier har da wanda ta caskara PSV Eindhoven 4-0 a Champions League ranar Laraba.

Wasa na biyu kenan da Gunners ta raba maki a babbar gasar tamaula ta Ingila, wadda ta fara yin 2-2 da Fulham a Emirates ranar 26 ga watan Agusta.

Ita ma dai Tottenham ba ta yi rashin nasara ba daga karawa shida da ta yi a Premier League ta kakar nan, wadda ta yi 2-2 a gidan Brentford ranar 13 ga watan Agusta.

Wasan da suka buga a bara 2022/2023

Premier League Lahadi 15 ga watan Janairun 2023

  • Tottenham 0 - 2 Arsenal

Premier League Asabar 1 ga watan Oktoban 2022

  • Arsenal 3 - 1 Tottenham

Ranar Laraba 27 ga watan Satumba, Gunners za ta ziyarci Brentford domin buga League Cup.

Kwana uku tsakani Bournemouth za ta karɓi bakuncin Arsenal a karawar Premier League.

Wasa biyun da ke gaban Tottenham kuwa shi ne wanda za ta karɓi bakuncin Liverpool ranar Asabar 30 ga watan Satumba.

Mako ɗaya tsakani Tottenham ta je Luton buga gasar Premier League fafatawar mako na takwas.