Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An janye ƙarar da aka shigar kan shugaban Fifa
Masu gabatar da ƙara sun rufe binciken da aka buɗe kan shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Gianni Infantino.
An buɗe bincike kan Infantino ne a watan Yulin 2020 kan wani taron sirri da ake iƙirarin ya yi da babban mai shari'ar Switzerland Michael Laurer.
Masu gabatar da ƙara a Switzerland sun tabbatar a ranar Alhamis cewa binciken da suka gudanar ya kawar da duk wani zargin da ake yi wa Infantino.
Infantino ya ce an ɓullo da wannan lamarin ne don a ɓata masa suna.
An buɗe binciken kan zargin Infantino da cin zarafi da amfani da ƙarfin ofishinsa a waɗansu tarurrukan da ya yi da Laurer.
Masu gabatar da ƙara sun ce binciken da suka gudanar bai gano wata shaida da ke nuna cewa Infantino ya tunzura ofishin babban mai shari'ar ƙasar Switzerland ko aikata ba daidai ba.