Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Labarai masu sosa rai na mutanen da aka kashe a Gaza
- Marubuci, Ethar Shalaby
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
- An wallafa
Adadin mutanen da suka mutu a gaza na ci gaba da ƙaruwa, yayin da isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare kan Hamas, bayan harin da ƙungiyar ta kai Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, inda mutum 1,400 suka mutu.
Ma'aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce fiye da mutum 9,000 ne aka kashe tun bayan fara yaƙin.
Sakamakon fargabar kariya, ƴan jarida ƙalilan ne suka samu zuwa Gaza domin tattara bayani kan irin ɓarnar da yaƙin ya haifar.
To amma BBC ta riƙa yin magana da iyalai da shaidun gani da ido waɗanda suka faɗa mana labaran ƴan uwa da abokan arzuƙansu da aka kashe a hare-haren.
Yusof Abu Mousa
Yayin da ake fuskantar matsalar rashin wutar lantarki a Zirin Gaza, Yusof, mai shekara bakwai tare da ƴan'uwansa biyu - Jury mai shekara 3 da Hamed mai shekara tara - sun yi sa'a.
Mahaifinsu, Mohamed Abu Musa - wanda likita ne mai ɗaukar hoton cutukan marasa lafiya a asibitin Nasser da ke birnin Khan Younis - ya saka musu wutar lantarkin sola mai amfani da hasken rana a gidansu, don haka yaran kan kalli tashoshin da suka fi so a talabijin.
Suna gaban akwatin talabijin ranar 15 ga watan Oktoba, a lokacin da mahaifinsu ya ce harin da Isra'ila ta harbo ta sama ya faɗa wa gidansu.
Jury da Hamed sun tsira da rayukansu, amma Yusof ya mutu bayan da rufin gidansu ya fado kansa.
Mohamed na tsaka da aiki a asibiti a lokacin da matarsa, Rawan, ta je asibitin tana kururuwar neman ƙaramin ɗan nasu.
Ita ta samo Hamed, yayin da tawagar masu aikin ceto suka zaƙulo Jury daga cikin ɓaraguzan gidan nasu.
Jury ta samu munanan raunuka a kanta, to sai dai iyayen nata sun ce tana 'samun sauƙi'.
Bidiyon yadda matarsa ta je asibitin a rikice tana neman 'ɗan lelen' ɗan nata ya karaɗe shafukan sada zumunta.
Daga baya ne Mohamed ya gano gawar ɗan nasu a sashen ajiye gawarwaki na asibitin.
"Rabuwarmu ta ƙarshe da Yosuf shi ne lokacin da zan tafi aiki, ya taho da gudu ya rungume ni a bakin ƙofar gidanmu", in ji Mohamed.
"Ya sumbace ni, sannan ya ce min: baba sai ka dawo, bayan na ba shi biskit da ayaba. Burinsa shi ne ya zama likita, watakila saboda kullum yana gani na ina tafiya asibiti."
Dakta Midhat Saidam
Da maraicen ranar 15 ga watan Oktoba, Dakta Saidam na buƙatar samun hutu. Likitan - da ke tiyata a asibitin al-Shifa - ya shafe fiye da mako guda yana aiki a asibitin da ke birnin Gaza.
Wata rana sai ya faɗa wa abokan aikinsa cewa yana son zuwa gida ya kwana.
Amma cikin daren ya mutu sakamakon wani hari ta sama da ya faɗa gidansa.
"Ya ce mana zai je gida ya kwana don ya samu barci ya huta, saboda gajiyar aiki, amma da safe zai dawo, sai dai kash! da safen gawarsa ce ta dawo," in ji Dakta Adnan Albursh, abokin aikinsa.
Dakta Albursh - wanda ya yi aiki da Dakta Saidam fiye da shekara 20 - ya ce suna yi wa abokin nasu laƙabi da "agogo sarkin aiki" saboda jajircewar shi.
Matasan likitoci na kallon Dakta Saidam - wanda jajirtaccen likita ne a ɗakin tiyata - a matsayin uba a fannin aiki.
"Duk wanda ya samu wata matsala a lokacin aikinsa, Dakta Saidam zai kira domin warware masa matsalar," in ji shugaban sashen tiyata na asibitin Ahmed El Mokhallalati.
"Mutuwarsa babban rashi ne ba ga asibitin kaɗai ba, har ma ga fannin aikin lafiya baki ɗaya," in ji shi.
Nour Yousef al-Kharma
A ranar 11 ga watan Oktoba aka kashe Nour - wadda ɗaliba ce mai shekara 17 - a lokacin wani hari ta sama da Isra'ila ta kai ya faɗa kan gidansu a garin Deir al-Balah, mai nisan kilomita 14 daga birnin Gaza, kamar yadda kawunta ya bayyana.
Mohammed al-Kharma ya ce ƴar ɗan'uwan nasa ta ƙuduri aniyar komawa wajen dangi a wani wurin na daban, sakamakon yawaitar hare-hare ta sama a garin.
"Mahaifinta ya buƙaci ta zauna a gidanta, amma washe gari da safe bam ya faɗa wa gidan. A haka ƙaddararta ta zo," in ji kawun nata.
An kashe Nour tare da ɗan baffanta Yazan, ƴan'uwan biyu sun yi ta wasa da juna a falon gidan. Manyan yayyinta biyu, Ola da Huda, - waɗanda ke ɗakin girki suna haɗa abin karin kumallo tare da mahaifiyarsu, Jamalat - sun tsallake rijiya da baya a harin.
Nour na ajin ƙashe a makarantar sakandire, kuma fatanta shi ne zama likita.
Kawun nata ya ce ƴan'uwansa sun zaƙulo jakar makarantarta daga cikin ɓaraguzan ginin gidan bayan ya rushe.
Akwai litattafan karatunta da wani ƙaramin kundin da take rubuta muhimman abubuwan da suka shafi rayuwarta.
Ɗaya daga cikin abin da ta rubuta a cikin kundin shi ne: "Ina da burin sanya dangina alfahari, kuma zan samu maki mai daraja da yardar Allah."
Lurin Azzam Abuhalima
Cikin saƙo na ƙarshe ta da aike wa saurayinta Khaled al-Masry, Lurin ta ce ta gaji da guje-gujen neman mafaka saboda yaƙin.
Lurin, mai shekara 30 ta taɓa komawa da zama a sansanin ƴan gudun hijira na Nusairat, da ke tsakiyar Zirin Gaza, domin zama tare da gwaggonta.
Sau biyu Lurin na tsallake rijiya da baya sakamakon hare-hare, ciki har da wanda ya fada kan ginin gidansu a birnin Gaza.
"Ta faɗa min cewa za ta je ta yi wanka ta yi salla, sannan ta kwanta", in ji saurayinta Khaled.
Saurayin nata ya ce tana salla a lokacin da harin ya faɗa kan gidansu.
"Tana tsaka da salla a lokacin da aka kashe ta", in ji saurayin.
An ɗage auren masoyan biyu zuwa Disamba a baya-bayan nan sakamakon yanayin da ake ciki a Gaza.
Fekriya Hassan Abdul A'al
Mazauna gundumar Radwan a birnin Gaza da ke bukatar tufafin mata, kan nufi shagon Fekriya Hassan Abdul A'al.
"Ina tuna lokacin da gidanmu ke cika da ƴan matan da ke shirin yin aure da ƙawayensu da ke zuwa domin sayen tufafin aure a wajen mahaifiyarmu," in ji ƴarta Nevine.
An kashe matar, mai shekara 65 - wadda tsohuwar tela ce - tare da ƴan'uwanta biyu da ƴaƴanta biyu da jikokinta biyu, bayan wani hari ta sama ya faɗa gidan da suke zaune ranar 23 ga watan Oktoba.
Mazen da Ahmed Abu Assi
Mazen mai shekara 17 da Ahmed mai shekara 13 - waɗanda ƴan'uwan juna ne - na daga cikin mutanen da suka mutu a wata fashewa da ta auku a asibitin al-Ahli ranar 17 ga watan Oktoba.
Jami'an Falasɗinawa sun ce fashewar ta auku ne sakamakon wani hari ta sama da Isra'ila ta kai.
To amma rundunar sojin Isra'ila ta ce lamarin ya auku ne sakamakon wani roka da wata ƙungiyar mayaƙan Falasɗinawa masu iƙirarin jihadi ta harba, zargin da ƙungiyar ta musanta.
Arafat Abu Massi - wanda shi ne mahaifin yaran biyu - ya ce yaran nasa ''aminan juna ne" amma halayensu sun bambanta.
Sai da aka yi wa Arafat da matarsa dashen kwan haihuwa na tsawon shekara takwas kafin su haifi Mazen - wanda ke makarantar sakandire, tare da fatan zama likitan haƙori.
"Ya fi kowa ƙwazo a cikin ƴaƴana," in ji shi.
"Yakan sayar da kayan wasan yara da na karatu a wani ƙaramin shago da ke kusa da gidanmu", in ji mahaifin.
A yanzu ƙaramin ɗansa mai shekara uku Faraj ne kawai ya rage masa.
Arafat ya ce a kullum Faraj kukan kewar ƴan'uwansa yake yi.
Salam Mema
An kashe ƴar jarida Salam Mema, mai shekara 32, ranar 10 ga watan Oktoba lokacin da wani hari ta sama ya faɗa gidanta da ke Jabaliya a arewacin Gaza, kamar yadda ƙawarta ta shaida wa BBC.
Mijinta, da ƴaƴansu biyu, Sham mai shekara biyu da Hadi mai shekara bakwai, da wani ɗan'uwansu, duka sun mutu a harin, inda suka bar ɗansu Ali mai shekara biyu.
A ranar 31 ga watan Oktoba, Salam na ɗaya daga cikin ƴan jarida 31 da aka tabbatar da mutuwarsu a rikicin Isar'ila da Hamas tun bayan fara yaƙin.
Safaa Nezar Hassouna
An kashe masaniyar harkokin magungunan a wani hari ta sama da aka kai birnin Rafah da ke kudancin Gaza, ranar 17 ga watan Oktoba.
Tana kwance a kan gado tare da ƴarta Elyana, ƴar watanni uku da kuma mijinta.
Kawun Safaa, Omar Hassouna - wanda tsohon likita ne da ke zaune a Birtaniya - ya ce iyayenta waɗanda suka tallake rijiya da baya a harin sun kaɗu da mutuwarta.
Omar ya ce lokaci na ƙarshe da ya gan ta shi ne lokacin da ya je hutu Gaza.
"Safaa na da faran-faran da mutane, mai taimakon jama'a, kuma mai farin jini a wajen kowa", in ji shi.
"Haƙiƙa na yi rashin ƴa. Na ji takaicin mutuwarta, kamar yadda na ji takaicin mutuwar sauran fararen hula a gaza".