'Aikin jigilar marasa lafiya na gudana cikin yanayi mai ban tsoro a Gaza'

.

Asalin hoton, JAKE MORLAND

Bayanan hoto, Motocin daukar marasa lafiya
    • Marubuci, By Frank Gardner
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC security correspondent in Jerusalem
  • An wallafa

Jake Morland, wani ɗan Birtaniya da ke aiki a ofishin kula da ayyukan jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA), ya shaidawa BBC cewa ana aikin jigilar marasa lafiya cikin yanayi na tashin hankali a Gaza.

A ranar asabar, 9 ga watan Disamba, wani ayarin motocin daukar marasa lafiya na hukumar lafiya ta duniya da MDD da ƙungiyar agajin Falasdinu da kuma wata babbar mota sun dauki hanya daga gabashin Gaza domin kai kayan asibiti daake tsananin buƙata a asibitin al-Ahli dake arewacin Gaza, tare da dauko wasu daga cikin marasa lafiya masu tsananin jin jiki zuwa asibiti a kudanci.

Kafin ayarin ya samu zuwa asibitin al-Ahli sai da ya je wajen shigen bincike na sojojin Isra'ila dake Wadi Gaza.

"Abin da muka yi tsammani shine duk shingen binciken da za a iske akwai izinin wucewa da ake ba ma'aikatan jin ƙai da kuma kayan agaji" inji Mista Morland wanda ya yi aiki da hukumar jin ƙai ta MDD a Gaza.

Sai dai wannan lokacin ya ce " Bayan mun tunkari sojojin dake bisa tulluwar ƙasar da suka tare hanya da ita da makamansu da suke cikin shirin kota kwana, wanda suka nuna mu da su."

"Daga baya mutum biyu cikinmu sun fita wajen sojojin domin amsa tambayoyi, sai dai, mun fahimci an tsaresu tare da sanya su rage tsawonsu, haka muka samu daƙyar aka sakesu muka wuce Gaza" Inji Mista Morland.

"Dukkan wannan yunƙurin kai kayan agajin an tsarasa ne a fili da kuma sanin sojojin Isra'ila, saboda mun basu dukkan bayanan kayan da muke dauke da su da kuma sunayen ƴan ayarin, kawai abin da muka fahimta shine ba a amince a yi wa Falasdinawa magani ba.

.

Asalin hoton, JAKE MORLAND

Bayanan hoto, Gaza

Daga Wadi Gaza, ayarin motocin ma'aikatan jin ƙan suka nufi Zirin Gaza, tsohon birnin wanda mista Morland ya ce yana cike da ɓuraguzan ginenen da suka rushe, wato dai wajen ya zama kufai.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"An harbe mu, motar daukar marasa lafiya an harba mata harsasai kamar yadda aka harbi babbar motar da ke dauke da kaya, hakan ya saka rayuwar masu ayyukan jin ƙai suma suna neman masu cetonsu.

A hanyar komawar ayarin motocin zuwa kudanci, nan ma na riƙa tsayar da su a wajen shingen binciken sojojin Isra'ila, duk da sun ɗauko marasa lafiya 19 dake tsananin jin jiki.

"Dukkan marasa lafiyar na dauke da manyan raunuka kuma suna jin jiki, suna kuma buƙatar agajin gaggawa, amman a haka aka tsayar da mu tsawon sa'a biyu ana tantancemu " in ji mista Morland.

"Kananan yaran da suka ji rauni ma sai da aka fito da su aka tsayar da su tsawon sa'a guda ana daukar hotunansu."cewar mista Morland

Daga ƙarshe dai, da dare ya yi kuma ƙarar makamai masu linzami na ƙara matsowa kusa da ayarin motocin, sai ayarin mutanen suka dauki mataki mai hatsari da wahala, inda suka bar ɗaya daga cikin ma'aikatan jinya wanda yanzu haka sojojin Isra'ila ke ci gaba da tsare shi," Muna tare da majinyatan da ke gaf da mutuwa saboda ɓata mana lokaci da sojojin Isra'ila suka yi" in ji Morland.

"Na samu labarin ɗaya daga cikin marasa lafiyar ya rasu kafin motarsu ta ƙarasa zuwa asibiti a kudanci. Mu na tunanin za a iya kaucewa faruwar hakan inda an bamu hanya cikin sauƙi.