Alƙalan wasa za su riƙa maƙala kyamara a jikinsu a gasar Club World Cup

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Alƙalan wasa za su riƙa maƙala kyamara a jikinsu a gasar kofin zakarun nahiyoyi, wato Club World Cup da za a yi a bana.

Za ake bai wa masu nuna gasar, domin watsa abubuwan da kamara ta dauka a sabuwar fasalin wasannin da ƙungiya 32 za ta barje gumi a tsakaninsu.

Shugaban raflin Fifa, Pierluigi Collina ya ce ''Dama ce don bai wa masu kallo sabuwar ƙwarewa, dangane da abubuwan da aka ɗauka daga kusurwar hangen nesa wanda ba a taɓa yin hakan ba."

Jarred Gillett, shi ne na farko da ya ɗaura kamara a lokacin Premier League, inda Crystal Palace ta doke Manchester United 4-0 a Mayun 2024.

An yi hakan ne a Premier a karon farko, domin samun hotuna da bidiyo, domin bai wa rafli bita kan alkalancin Tamaula.

Chelsea da kuma Manchester City suna daga cikin masu buga Premier League da za su kara a tClub World Cup da za a fara daga 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli.