Yadda Mohamed Salah ya ɓace ɓat a wasa da Newcastle

Asalin hoton, PA Media
Hutun gasar lig lig da za a tafi a makon nan zai zo wa Liverpool da mafita bayan rashin nasarorin da ta yi fama da su a jere, musamman a wasan ƙarshe na Carabao Cup da Newcastle.
Kafin Newcastle ta warce kofin na Carabao bayan cinye Liverpool 2-1 a filin wasa na Wembley, PSG ta Faransa ce ta fara fitar da ita daga gasar zakarun Turai ta Champions League kwana biyar da suka wuce.
An yi tunanin tawagar Arne Slot za ta manta da abin da ya faru a wasan na PSG, amma kuma sai suka nuna gajiyawa a wasa da Newcastle fiye da wadda suka nuna a PSG.
Duk da cewa Newcastle ta ɗan sha wuya a ƙarshen wasan bayan Federico Chiesa ya farke ƙwallo ɗaya, ƙwallayen da Dan Burn da kuma Alexander Isak suka ci ne suka ba ta damar lashe kofin.
Babbar tauraron ɗanwasan na Liverpool, Mohamed Salah, bai nuna yana cikin wasan ba, inda ya gaza taɓuka komai duk da irin ƙwallayen ya zira a kakar bana.
Salah ya ci wa Liverpool ƙwallo 32 a dukkan gasanni a kakar bana tare da bayar da 22 a zira a raga. Shi ne kan gaba a yawan cin ƙwallo a Premier da 27, sai Haaland mai 21, da Isak na Newcastle mai 19 a raga.
Bayan gaza taɓuka abin kirki a wasa da PSG, ɗan ƙasar Masar ɗin ya sake gajiyawa a daidai lokacin da Liverpool ke buƙatarsa, kuma hakan ne ke nuna ƙungiyar ma gaba ɗayanta ba ta yi ƙoƙari ba.
Ko shot ɗaya bai buga ba

Asalin hoton, PA Media
A wasa da Newcastle, da Salah aka fara kuma da shi aka tashi. Ya taɓa ƙwallo sau 23, inda ya bayar da fasin 17 jimilla, amma 13 ne suka je inda ya aika su.
Kazalika, bai buga shot ko ɗaya ba, sau biyu ya bugo ƙwallo cikin yadi na 18 daga gefe wato kurosin amma ɗaya ce ta je, kuma sau ɗaya ya yanka ɗanwsan Newcastle.
Haka nan, sau ɗaya ya taɓa ƙwallo a cikin yadi na 18 na Newcastle.
Duk da cewa ba shi ne babban aikinsa ba, Salah bai ƙwaci ƙwallo daga ƙafar 'yan Newcastle ko sau ɗaya ba, amma ya dawo da ƙwallon ƙafarsu sau biyu, kuma sau ɗaya aka yi masa ƙeta.
Liverpool ta yi ta fatan lashe kofuna huɗu a bana tun bayan da ta ɗare saman teburin Premier League da na Champions League, sai kuma Carabao da FA, amma yanzu Premier ne kaɗai ya rage mata bayan fitar da ita a duka gasannin.
Ita ce ta ɗaya a Premier da maki 70, sai Arsenal mai biye mata da maki 58, yayin da ya rage mata wasa tara kafin kammala gasar.











