Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arteta ya ce Saliba zai murmure ya fuskanci Man City a Premier
Watakila William Saliba ya buga wa Arsenal wasan Premier League da Manchester City ranar 2 ga watan Fabrairu, in ji Mikel Arteta.
Rashin Saliba ya sa Gunners ta kasa samun maki uku a kan Aston Villa ranar Asabar, wadda ta fara cin ƙwallo biyu daga baya Villa ta farke su.
Hakan ya sa Liverpool mai jan ragamar teburin Premier ta bai Gunners tazarar maki shida, kuma tana da kwantan wasa da Everton.
Arteta ya sanar cewar Saliba ba zai yi wa gunners karawar Champions League ba da Dinamo Zagreb ranar Laraba, amma yana sa ran zai fuskanci City a Premier.
Arsenal na fuskantar kalubale a gurbin mai cin ƙwallaye a bana, Kai Havertz baya yin abinda ake bukata - hakan ya sa Gunners ke fatan shiga kasuwa a Janairun nan.
Rashin wasu daga manyan Arsenal a gasar zakarun Turai da za ta buga ranar Laraba, ya sa ta kara gayyatar Ethan Nwaneri da kuma Riccardo Calafiori.
Idan Arsenal ta doke Dinamo Zagreb ranar Laraba zai bata damar zama cikin gurbin masu zuwa zagayen gaba kai tsaye.
Yanzu dai Arsenal tana ta ukun teburi a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai, bayan cin wasa huɗu da canajaras da rashin nasara ɗaya.